Labarai

Yadda aka sace mata kimanin Arba’in a Borno

Yadda aka sace mata kimanin Arba'in a Borno

A daren Alhamis ne, ƴan bindiga waɗanda ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka sako matan da suka sace daga wani ƙauye na ƙaramar hukumar Jere a jihar Borno.

 

Matan sun isa gida ne cikin tsakiyar dare da ƙyar, cike da gajiya, jigata kuma a galabaice.

 

Borno, na cikin jihohin da suka fi fama da rikicin Boko Haram, wanda ya yi sanadin mutuwar ɗumbin mutane da raba miliyoyi da gidajensu a ƙasashen Najeriya da Nijar da Kamaru har ma da Chadi.

 

A shekarun 2010, an bayyana Boko Haram a matsayin mafi hatsari cikin ƙungiyoyi masu ayyukan ta’addanci na duniya.

 

Ƙungiyar, wadda gwamnatin Najeriya da ta gabata ta yi iƙirarin cin galabarta, kan yi amfani da satar mutane a matsayin wata dabara ta jan hankalin hukumomi ko kuma neman kuɗi.

 

Garkuwa da mutane mafi shahara da ƙungiyar ta yi, ita ce ta ɗalibai 276 daga sakandiren ‘yan mata ta Chibok a watan Afrilun 2014, waɗanda har yanzu ba a gama karɓo su ba.

APPLY NOW!  Wace illa juyin mulkin Nijar zai yi wa duniya?

 

A wannan karo salon garkuwa da matan na ƙauyen Maiwa ya fi kama da na neman biyan buƙata ta kuɗi.

 

Wani da ya shaida lokacin da matan suka isa gida bayan sako su, ya ce akwai waɗanda suka dawo da raunuka a jikinsu, yayin da wasu ke cikin halin rashin lafiya.

 

Ɗaya daga cikin matan da aka sako, bayan sace su ranar Talata, mai suna Talatu (Ba sunanta na gaskiya ba ne), wadda ke cikin tsananin gajiya kuma ƙarfinta ya ƙare, ta ce tun da aka ɗauke su ba su ci komai ba, sai ruwan taɓo kawai da suke sha.

 

“Mun yi tafiya ta kai ta awa biyar, tun da muka je ba mu ci komai ba, sai ruwan da ke kwance a ƙasa suka ɗiba suna ba mu.”

 

Ta ce “Yanzu haka da ƙyar nake magana da kai, ga mu nan, ba mu san yadda za mu yi ba.”

APPLY NOW!  Su wane ne kusoshin gwamnatin Tinubu?

 

Talatu ta faɗa wa BBC cewa an ɗauke su ne da misalin ƙarfe 11 na safiyar Talata a lokacin da suka je daji domin nemo itacen girki.

 

Ta ce: “Mu ne ke zuwa neman itace saboda idan mazanmu suka je kashe su ake yi.

 

“A lokacin da muke tafiya sai suka ɓullo mana, wasu kuma suna kan bishiya, suna da yawa, suna sanye da kayan gida amma suna ɗauke da bindigogi.”

 

Akasarin mazauna jihar Borno, manoma ne ko ƙananan ma’aikata da kuma masunta.

 

A shekarun baya-bayan nan, an sha samun rahoton yadda ƙungiyar Boko Haram take kashe mutane a gona ko a wuraren kamun kifi.

 

Ƴan bindigan sun tafi da Talatu da sauran mata da aka ƙiyasta yawansu ya kai 48.

 

Mayaƙan da suka sace su Talatu, sun shaida musu cewa sun ɗauke su ne domin suna buƙatar kuɗi, kuma sun ce ba za su sake su ba, sai an biya fansa.

APPLY NOW!  An Kama Bama Bamai Guda 399 NDLEA

 

Bayan kimanin wuni guda ƙalilan daga cikin matan sun samu nasarar tserewa daga hannun ƴan bindigar, inda suka koma gida.

 

Talatu ba ta san yawan kuɗin da aka tara ba, amma ta ce dattijan garin ne suka kai kuɗin fansa kafin a sako su.

 

Ta ce: “An tara kuɗin ta hanyar rance da ma duk wata hanya da za a iya samu, sai dattijai suka kai.

 

“Sun sake mu a cikin daji, da ƙyar muka dawo, saboda wasu ba su da lafiya, wasu kuma sun gaji saboda yunwa.”

 

Ƙauyen dai yana wani yanki ne kusa da Maiduguri, babban birnin jihar da nisan ƙasa da kilomita 20.

 

Har yanzu akwai dakarun sojin Najeriya jibge a jihar Borno, wadanda ke aikin kakkaɓe ragowar mayaƙan ƙungiyar Boko Haram da kuma na Iswap.

 

Wata majiyar tsaro ta ce dakarun da ke jibge a kusa da ƙauyen na aikin samar da tsaro ga manoma, kasancewar an samu raguwar kai hare-hare a garuruwa da ƙauyuka.

APPLY NOW!  Ɗalibin Sheikh Abduljabbar yayi mafarki da Sheikh Ibrahim Inyass tare da Manzon Allah.

 

To amma, har yanzu akan samu hare-hare nan da can a dazukan jihar.

 

Bayani sun nunu cewa matan da aka sace a ranar ta Talata sun yi nisan zango ne, inda suka zarce yankunan da sojoji kan yi sintiri domin bayar da tsaro ga masu zuwa gonaki.

 

Me hukumomi suka ce?
Har yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnati ko jami’an tsaro game da batun.

BBC ta yi yunƙurin tuntuɓar gwamnatin jihar Borno sai dai lamarin ya ci tura.

Ɗaya daga cikin jami’an gwamnatin ya ce ba shi da masaniya kan lamarin don kuwa a yanzu haka yana ƙasar waje, sannan duk yunƙurin da muka yi na samun kwamishiniyar mata ta jihar Borno, bai kai ga nasara ba.