Labarai

Laifin Me Maryam Shatty Tayi Aka Cire ta a minista??

Laifin Me Maryam Shatty Tayi Aka Cire ta a minista??

Maryam Shatty: Shin Me Ta Tare Wa Wasu Ne?

 

Wannan baiwar Allah ta samu sunanta ya bayyana cikin jerin Ministocin da Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya zayyana a gwamnatinsa.

 

Wani abin mamaki shi ne, ana samun labarin, sai aka tarbe shi da mabanbantan ra’ayoyi. Wasu, musamman masoya da abokan arziki, sai suka shiga murna da addu’o’in taya murna. Wasu kuma nan take suka shiga kushewa da baƙaƙen magana a kan Hajiya Maryam.

APPLY NOW!  CIN AMANA A YAKI DA TA'ADDANCI A NIGERIA

 

Ni kuwa Shanshani, sai abin ya ɗaure mani kai. Shin me zai sa abin alheri zai samu mutum amma maimakon a taya shi murna, a ƙarfafe shi, a ba shi shawarar kirki amma sai a koma kishi da hassada da baƙin ciki?

 

Shin laifin me ta yi maku? Shin me ta tsare maku? Lallai ya kamata mu shiga taitayinmu, mu kama kanmu, mu yi abin da ya kamata. Mu sani cewa hassada babu abin da take haifarwa sai asarar da asara da asara.

APPLY NOW!  Menene gaskiyar labarin da ake yadawa, na farashin Man Fetur zai koma Naira 250 ko 300 a sati mai zuwa?

 

Maryam Shatty dai Allah Ya sanya ta cikin jerin Ministocin Najeriya. Babu abin da wani zai iya yi. Allah Ya ƙaddara abin da ya shirya a rayuwarta. Muna roƙon Allah Ya kama hannunta, Ya yi mata jagora. Ba ita kaɗai ba, har da sauran dukkan shugabanninmu. Allah Ya ba su ikon yin abin da ya kamata na alheri.

APPLY NOW!  Yanzunnan Tinubu Ya Bayyana Labari Medadi Ga Yan Nigeria Kan Tallafin Man Fetur

 

Amin

Advertisement