Labarai

An kama ‘Yar Leken Asirin ’Yan Bindiga

An kama 'Yar Leken Asirin ’Yan Bindiga

’Yan sanda sun kashe dan bindiga daya tare da cafke wata mata da ke yi wa ’yan bindiga leken asiri a Jihar Zamfara.

 

Rundunar ’yan sandan jihar ta sanar da cafke matar ne bayan jami’anta sun dakile harin ’yan bindiga a babban caji ofis da ke Karamar Hukumar Zurmi a jihar.

 

Kakakin rundunar, ASP Yazid Abubakar ya ce ’yan bindigar sun gamu da gamonsu a hannun ’yan sanda ne bayan ’yan sanda sun kai harin ofishin, amma ’yan sanda suka ce da wa Allah Ya hada su in ba su ba.

Bayan musayar wuta na sa’o’i ’yan bindigar suka jefar da bindigogi kirar AK47 guda biyu da babur dinsu suka tsere suka jefar da babur dinsu.

 

Bayan nan ne a yayin binicike ’yan sanda suka kama wata mata mai shekara 35 daga kauyen Rukudawa da ta amsa cewa ta dade tana wa ’yan bindiga leken asiri kuma jagoran ’yan ta’adda mai suna Dankarami Gwaska, ne ya sa ta leken asiri a ofishin ’yan sandan.

 

“An samu wayayo biyu dauke da lambobin ’yan ta’adda a hannunta,” in ji ASP Yazid Abubakar.

 

Ya ce a ranar Juma’a 28 ga watan Yuli kuma ’yan bindiga sun yi yunkurin kai hari a yayin da ake Sallar Juma’a a yankin Magarya na karamar hukumar Zurmi, amma ’yan sanda suka dakile su, suka tsere suka bar makamansu

“A ranar 27 ga watan kuma ’yan sanda sun samu bayanan sirri da suka yi amfani da su wajen cafke wasu ’yan bindiga biyu da suka addabi yankin Saminaka da ke garin Gusau