Labarai

Gwamnan ya ba da umarnin raba shinkafa buhu 40,000 don rage radadi

Gwamnan ya ba da umarnin raba shinkafa buhu 40,000 don rage radadi

Gwamnan jihar Katsina, Umar Dikko Raɗɗa ya ce ya ba da umarnin raba shinkafa buhu 40,000 nan take, ga al’ummar jihar da nufin rage raɗaɗin matsin rayuwa bayan cire tallafin man fetur a Najeriya.

 

Wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Gwamna Raɗɗa ya ce gwamnatinsa ta sayo shinkafar ne daga kuɗin rage raɗaɗi da jihar ta karɓa daga gwamnatin tarayya.

APPLY NOW!  Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Wa Dakarun Ta Kashedi

Ya kuma ce ya amince da kafa kwamitoci don raba shinkafar a matakan ƙananan hukumomi da mazaɓu na jihar.

Sai dai, saɓanin naira biliyan biyar da Majalisar kula Tattalin Arziƙin Ƙasa ta ambata tun farko bayan wani taro da ta gudanar kwanan baya, Gwamna Umar Raɗɗa ya ce gwamnatinsa ta sayo shinkafar ne da naira biliyan biyu da gwamnatin tarayya ta saki.

APPLY NOW!  Anfani da fetur a Najeriya ya ragu kashi 35 cikin 100

Haka zalika ya bayyana kafa kwamitocin bibiya da sa ido don ganin yadda aikin rabon shinkafar zai kasance.

Umar Dikko Raɗɗa ya kuma yi gargaɗin cewa duk mutumin da aka samu da ƙoƙarin cin amana a aikin rabon shinkafar, kai tsaye ko a kaikaice, to zai fuskanci fushin hukuma.