Labarai

An Kuma: Sojojin Gabon sun ce sun yi juyin mulki

An Kuma: Sojojin Gabon sun ce sun yi juyin mulki

Sojoji sun bayyana a gidan Talabijin na ƙasar Gabon, inda suka bayyana cewa sun ƙwace mulki.

 

Sun ce sun soke zaɓen da aka yi na ranar Asabar da aka bayyana Shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

 

Hukumar zaɓe ta bayyana Mr Bongo a matsayin wanda ya lashe zaɓe da kashi biyu cikin uku na ƙuri’un da aka kaɗa amma ƴan adawa sun ce an tafka maguɗi.

 

Wannan matakin ya kawo ƙarshen shekara 53 da aka shafe iyalan gidan Bongo na mulki a ƙasar Gabon.

 

Sojoji 12 sun bayyana a Talabijin inda suka sanar da soke zaɓen tare da rushe “duk cibiyoyin gwamnati”.

 

Ɗaya daga cikin sojojin ya sanar a gidan Talabijin na Gabon 24 cewa “Mun yanke shawarar tabbatar zaman lafiya da kuma kawo ƙarshen wannan gwamnatin.”

 

Mr Bongo ya hau kan mulki ne bayan rasuwar mahaifinsa a shekara ta 2009.

 

Wane ne Ali Bongo?

Wasu na kallonsa a matsayin sangartaccen ɗa, wanda ke kallon mulkin ƙasar Gabon a matsayin hakkinsa na gado.

APPLY NOW!  Alqawura 6 Da Tinubu Ya dauka A jawabansa Na Jiya

 

Ya taba zama mawaki, inda daga baya ya gaji mahaifinsa a matsayin shugaban kasar, ya dora a kan shekara 50 da iyalansa suka kwashe suna mulkin kasar.

 

Wasu kuwa na masa kallon mai kawo sauyi, kuma sun ce talakawa ne suka zabe shi bisa tsari na demokuraɗiyya.

 

Sai dai rashin lafiyar da ya yi fama da ita a shekarun baya sun haifar da tantama a kasar mai yawan al’umma sama da miliyan biyu.

 

A ranar 7 ga watan Janairun 2019 wasu gungun sojoji sun yi yunkurin yi masa juyin Mulki, lamarin da bai yi nasara ba.

 

Sojojin sun ce dalilin yunkurin nasu shi ne domin su mayar da mulkin demokuradiyya a kasar bayan zaben shekara ta 2016, inda Mr Bongo ya yi nasara da kyar duk da zarge-zargen cewa an tafka magudi.