GWAMNAN KANO YAYI ABIN A YABA
Bugu da ƙari cikin zaman da majalisar zartarwa ta gudanar a jiya laraba karkashin jagoranci na, majalisar zartarwa ta amince da abubuwa kamar haka:
1- Mun saki kuɗi kimanin miliyan ɗari 8 da 54 (854m) domin fara gudanar da bikin auren zawarawa a jihar Kano.
2- Na naɗa kwamiti na musamman da duba yadda zamu biya dukkanin ƴan fansho dake jihar Kano haƙƙoƙin su.
3- Za’a sake gyara gadojin sama guda uku waƴanda suke taimakawa ɗalibai wajen shiga makarantun su a bakin ƙofar shiga tsohuwar jami’ar Bayero dake nan Kano, da kuma wacce take a bakin ƙofar shiga Kwalejin koyon ilimi addini ta Malam Aminu Kano hadi da gadar da ke ƙofar shiga makarantar koyon ilimi mai zurfi ta Sa’adatu Rimi. -AKY
Tabbas na yaba da wannan kyakkyawan yunkuri na Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf
Allah Ka tabbatar masa da kujeransa, Ka kareshi daga makircin jam’iyyar APC mayaudariya