Labarai

Makamin da Rasha ta harba ya kashe mutum 7 ya jikkata 144 –

Makamin da Rasha ta harba ya kashe mutum 7 ya jikkata 144 -

Mutum bakwai ciki har da wata yarinya ‘yar shekara shida sun mutu, yayin da Rasha ta harba wani makami mai linzami kan wani ɗakin wasanni a birnin Chernihiv da ke arewacin Ukraine da safiyar Asabar, kamar yadda hukumomin ƙasar suka bayyana.

 

Yan sanda sun ce yara 15 na cikin mutum 144 da suka raunata, yayin da aƙalla 25 ke asibiti suna karɓar magani.
Cikin mutanen har da mutanen da ke farin cikin hutun mabiya cocin Orthodox da ke wata coci a gefe.
A kwai wani katon dandali da wani ginin jami’a duka sun lalace yayin wannan hari.

 

APPLY NOW!  Gwamnatin Najeriya tayi bayani akan shiri na sake dawo da tallafin mai

Majalisar Ɗinkin Duniya ta kira harin da “mugunta” yayin da shi kuma Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya sha alwashin ramuwa daga sojojinsa kan wannan “harin ta’addanci”.

 

Garin Chernihiv na da nisan kilo mita 50 da iayakar Belarus daga kudancin Ukraine. A baya sai da dakarun Rasha suka yi masa ƙawanya a farkon mamayar da Shugaba Vladimir Putin ya yi wa Ukraine a watan Fabirairun 2022.

APPLY NOW!  Rashin hadin kan gwamnatoci dama ce ga Yan Bindiga

 

Harin ya dira ne kan ɗakin wasan mai ɗaukar ido kai tsaye.

 

Magajin garin Chernihiv ya shaida wa BBC cewa a lokacin ana wani taron masu haɗa jirgi maras matuƙi ne a ɗakin makamin ya sauka.

 

“Na fuskanci taron sojojin da ake yi a wurin shi suka nufa da wannan hari ba wai ɗakin taron ba kawai,” in ji Oleksandr Lomako

APPLY NOW!  Shugaban ECOWAS bola Tinubu ya sakawa Nijar Dokoki

 

“Amma daga dakarun Rasha har waɗanda suka ba su umarnin ƙaddamar da harin sun yi amannar cewa idan suka kai hari wurin zai fi shafar fararen hula ne.

 

“Babu wata hanya da za su iya haka sai dai a aikata laifukan yaƙi, a kashe fararen hula, muna da shi a ajiye, Rasha ta ƙara aikata wani laifin yaƙin,” ya ƙara da cewa.

APPLY NOW!  Yadda aka yi wa wasu 'yan mata tsirara a hotunan da AI ya kirkira

 

Ministan cikin gida na Ukraine Ihor Klymenko ya ce duka mutanen da suke cikin ɗakin sun halarci wajen a kan lokaci.

 

Ya ce “mafi yawa waɗanda abin ya rutsa da su, sun ma shiga ababan hawansu da suka ajiye a gefen titi lokacin da aka harbo makamin, wasunsu kuma suna dawowa daga coci”.

APPLY NOW!  Yanzunnan Tinubu Ya Bayyana Labari Medadi Ga Yan Nigeria Kan Tallafin Man Fetur

 

Tsakiyar birnin na Chernihiv waje ne da ya shahara kuma mutane kan zuwa shaƙatawa musamman a ƙarshen mako, kamar yadda wani ya shaida wa BBC.

 

Anna Zahreba, manajan wani gidan abinci ce da ke tsallaken inda aka kai harin, tace ma’aikatanta na shirin fara aiki lokacin da abun ya faru.

APPLY NOW!  Cristiano Ronaldo Yana Burin Zuwa Dakin Ka'aba

 

“Na fita waje a guje na ga mai yake faruwa,” in ji ta. “Na ga wata yarinya ‘yar shekara 12 cikin jini. Ɗaya daga cikin kafafunta ta jikkata sosai. Akwai wata yarinya a gefe ita kuma tana ta ihu

 

Mun ba su agajin gaggawa tukunna muka jira motar asibiti. Yana ɗaukarsu lokaci mai tsawo kafin su zo nan, amma daga baya wani mutum ya bayar da motarsa aka kaita asibiti.”

APPLY NOW!  Abu uku da manyan hafsoshin tsaron ECOWAS za su mayar da hankali

Anna ta ce ma’aikatanta sun rika taimakawa mutanen da suka jikkata da magani da kuma barguna.

A bayanin da yake yi na bidiyo, Shugaba Zelensky ya ce yarinyar da aka kashe a harin Rasha sunanta Sofia.

An dai fuskanci Rasha tana yawan kai hare-harenta ne a ranar kowacce Asabar, ta mayar da ranar ta damuwa da baƙin ciki.

APPLY NOW!  Ambaliyar Ruwa: Hukumomi Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutum Fiye Da 2,000 A Libya.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce wannan hari ya matuƙar “tayar mata da hankali”.

Tuni aka sanar da hutun kwanaki uku a birnin domin zaman makoki.

Har yanzu dai Moscow ba ta ce komai ba kan wannan batu.