Labarai

Abunda ya Faru Bayan Ansawa Nijar Takunkumi

Labari Da Dumi Dumi Akan Halin da Nijar take ciki

Mazauna sassan Jamhuriyar Nijar sun fara kokawa game da tsadar rayuwa da suka shiga sakamakon rufe iyakokin ƙasar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

 

Wasu ‘yan kasar musamman ‘yan kasuwa sun ƙara farashi kan kayayyakin masarufi, suna masu alaƙanta hakan da fara aiwatar da takunkuman da aka saka wa ƙasar sakamakon juyin mulkin na ranar Laraba.

 

Lamarin na faruwa ne yayin da mambobin ƙungiyar Ecowas ta raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma suka fara aiwatar da takunkumin daina hulɗar kasuwanci da Nijar.

 

Ƙasar Benin wadda maƙwabciyar Nijar ce ta ɓangaren arewaci ta rufe iyakarta.

 

Da ma tuni sojojin da suka kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum suka sanar da rufe iyakokin ƙasar ta ruwa da sama da kuma ƙasa ‘yan awanni bayan juyin mulkin.

Baya ga takunkuman da ta saka wa Nijar ɗin, Ecowas ta kuma bai wa sojojin ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani mako ɗaya don su mayar da Bazoum kan mulki.

Cikin matakan da ƙungiyar ta yi barazanar ɗauka har da na ƙarfin soja yayin taron da ta gudanar a Abuja ranar Lahadi.

A ranar Juma’a ne Janar Tchiani ya bayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa bayan rundunar da yake jagoranta ta dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa ta kifar da gwamnatin farar hula ta farko da ta karɓi mulki daga irinta a Nijar.

Tuni kayan masarufi suka fara yin tashin gwauron-zabi a Yamai babban birnin ƙasar, a cewar wakiliyar BBC Hausa Tchima Ila Issoufou’