Labarai

Sojojin Nijar sun amince da karban Sojojin Mali da Burkina Faso

Sojojin Nijar sun amince da tura sojojin Mali da Burkina Faso zuwa ƙasar Domin tayasu yaki da ECOWAS

Jagoran juyin mulki a jamhuriyar ta Nijar, Janaral Abdourahamane Tchiani, ya rattaba hannu kan wata doka da za ta bai wa Sojojin Mali da Burkina Faso tura dakaru zuwa ƙasar domin taimakawa wajen kare ƙasar daga harin ƙungiyar ECOWAS.

Sanarwar na zuwa ne lokacin da ministocin harkokin wajen Burkina Faso Olivia Rouamba da na Kasar Mali Abdoulaye Diop, suka kai ziyara Kasar Nijar a jiya Alhamis.

Kungiyar ECOWAS dai ta yi barazanar afka wa Nijar din domin mayar da ƙasar kan turbar Dimukradiyya ta hanyar amfani da karfin soji a KO wanne lokaci.

ECOWAS ta yi kira ga sojin juyin mulkin su saki shugaba Mohamed Bazoum da mai dakinsa da ɗan shi, da suke tsare da su, tun bayan hambarar da gwamnatinsa, a watan da ya gabata tare da maidashi Kan karagar Mulki.

Tun bayan Mutuwar shugaban Wagner hankalin Sojojin Nijar din ya Kara tashi domin sunsan Rasha bazata tura Sojojin ta Nijar BA da sunan yaki Suma kuma Wagner bazasu Shiga rigimar BA har sai anyi sabbin Nade naden jagoranci saboda harda manyan Kungiyar a cikin Wanda suka mutu a Hatsarin Jirgin Wanda shugaban Wagner din kanshi yake ciki.

APPLY NOW!  Alqawura 6 Da Tinubu Ya dauka A jawabansa Na Jiya