Labarai

Gwamnatin Tinubu Zata Bada Tallafi

Mihimman Alqawura shida da Tinubu ya dauka

Muhimmman abubuwa Shida (6) da na ciro su daga jawaban da shugaba Bola Ahmad Tinubu yayi jiya da Magriba ga ‘yan Nigeria:

 

1. Gwamnatin sa ta amince da rarraba Ton dubu Dari biyu (200,000 Tonne) na kowane kayan Abinci da Gwamnati take dasu domin ‘kokarin sauko da farashin kayan Abinci ko rage tsadar sa a cikin Nigeria.

 

2. Gwamnatin sa zata bayar da tallafin Naira Biliyan 50 wa masu Kananan Sana’o’i domin su ‘kara karfin Jarin su.

~ Mutane dubu 1,300 daga kowace karamar hukuma zasu samu Kudin, daga cikin Kananan hukumomi 774.

 

3. Daga yanzu zuwa kowane lokaci Gwamnatin zata ‘kara Albashi wa Ma’aikata a fadin kasar gaba daya, tare da habaka Mafi karancin Albashi (Minimum Wage) a lokaci guda.

 

4. Gwamnatin zata shigo da Motoci masu amfani da Gas (CNG) guda dubu uku a Sahun farko domin rarraba su a fadin kasar don rage sassauta wa mutane zirga zirgan abin Hawa.

APPLY NOW!  Shugaban ECOWAS bola Tinubu ya sakawa Nijar Dokoki

 

5. Gwamnatin zata bayar da Bashin Naira Biliyan 75 wa kamfanoni 75 don su Kara Jari kuma su dauki ‘yan Nigeria a matsayin Ma’aikata don rage yawan marasa aiki yi.

~ Daga yanzu zuwa watanni 9 masu zuwa za’a kammala bayar da Kudin wa kamfanonin, inda zasu biya cikin shekaru 2 bayan sun fara aiki da watanni 12 bayan karban Kudin.

 

6. Gwamnatin sa zata kashe Naira Biliyan Dari Dari 200 domin Noman Shinkafa Hectare dubu Dari 400,000 tare da Alkama da Noman Rogo.

 

~ Za’a fitar da Naira Biliyan 50 domin doman Alkama Hectare dubu 100,000 da Rogo Hectare dubu 100,000 a fadin Nigeria.

 

Allah ya tabbatar ya bada ikon yi, yasa abinda aka tsara ayi da gaskiya, Allah ya bada iko kayan suje hannun wadanda aka yi domin su, su kuma Allah yasa suyi domin cigaban kasar da tsayawa akan manufar da ake so ayi akai.

 

✍️:

A.I.I