Labarai

An daina jin ɗuriyar kumbon sama jannati da Indiya ta tura duniyar wata

An daina jin ɗuriyar kumbon sama jannati da Indiya ta tura duniyar wata

An daina jin ɗuriyar kumbon sama jannati da Indiya ta tura duniyar wata

...

ASALIN HOTON,ISRO

Amma sun ce za su ci gaba da ƙoƙari har zuwa ƙarshen rana ɗaya ta duniyar wata.

Kwana ɗaya a duniyar wata daidai yake da kimanin kwana 14 a duniyarmu.

Kumbon dai ya isa duniyar wata ne a watan Agusta. Kumbon ya kwashe mako biyu yana tattara bayanai da hotuna, inda daga bisani aka kashe na’urorin a lokacin da dare ya yi aduniyar ta wata.

A ranar Juma’a, hukumar ta wallafa a dandalin sada zumuntanta na X (tsohon Twitter) cewa “za su ci gaba da ƙoƙarin tura saƙonni zuwa kumbon”. Babu dai wani martani da aka samu daga kumbon zuwa yanzu.

Damar kumbon na Indiya da sake farkawa na raguwa saboda tsananin sanyi a duniyar wata, tare da yanayin zafi a maƙurar duniya ta kudu ya ƙaru daga 200C zuwa 250C.

Wane muhimmanci wannan shiri na zuwa duniyar wata ke da shi ga Indiya?

Indiya ta kafa tarihi lokacin da kumbon da ta aika ya sauka a maƙurar duniyar wata ta kudu.

...

ASALIN HOTON,ISRO

An shirya saukar kumbon na Indiya a daidai farkon rana a duniyar wata, yadda Vikram da Pragyaan za su sami hasken rana na makonni biyu don yin aiki.

Masana sun bayar da misali da kumbon Chang’e4 na kasar China da kuma Yutu2 rover wanda ya farfaɗo a karo da dama bayan fitowar rana.

Amma Isro ta ce idan Vikram da Pragyaan ba su farka ba za su ci gaba da zama a duniyar wata a matsayin jakadun Indiya a duniyar wata”.