Labarai

An yi ruwan saman da yakai shekara 20 cikin kwana daya a Libya

An yi ruwan saman da yakai shekara 20 cikin kwana daya a Libya

An yi ruwan sama ninki 260 na abin da ake samu tsawon wata guda a cikin sa’a 24 a Libya.

 

Madatsun ruwan sun fashe a Derna bayan gawurtacciyar guguwar Daniel ta auka wa Libya a farkon wannan mako, inda ya malalo ruwan saman da ba a taɓa gani a wasu yankunan gaɓar tekun ƙasar.

 

Guguwar ta taho da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya fiye da tsayin inci 16 kwatankwacin milimita 400 a yankunan gaɓar tekun cikin sa’a 24.

 

Ruwa ne mai yawan da ba a saba gani ba a yankin da galibi abin da ake samu bai fi milimita 1.5 ba kawai a ɗaukacin watan Satumba.

 

Ko, kuma dai kawai a ce fiye da ninki 260 na ruwan saman da akasari yake sauka cikin wata ɗaya, amma wannan karo a cikin kwana guda.

 

Bayanai daga tauraron ɗan’adam sun nuna yawan ruwan saman da aka yi a faɗin yankin – ko da yake a wasu wuraren ruwan da ya sauka ya fi yawa.

 

Ɓarna mafi muni da aka gani ta faru ne, sanadin bala’in ambaliyar ruwa bayan fashewar madatsun ruwa biyu a kan Kogin Wadi Derna.

 

Kogin Derna dai, akasari bai fiye cikowa ba, amma ruwan sama a wasu ‘yan lokuta yakan tumbatsa a madatsun.

 

Madatsun biyu suna tare ruwa mai yawan da ya kai nauyin tan miliyan ɗaya da rabi, sannan haɗuwar ƙarfin ruwan da ke kwarara da tarkacen da ya riƙa cin karo da su ne, ta ƙara munin ɓarnar da aka samu.

 

Shaidu sun ce ruwan ya kai kusan mita uku wato ƙafa goma a wasu wurare.

 

Gudun ambaliyar ruwan da ya kai tsawon inci shida, ya isa ya tunkuɗe mutum ƙasa, haka zalika ruwa mai tsawon ƙafa biyu kawai yana iya ɗaga mota ya tafi da ita.

Mutane fiye da 20,000 ake fargabar sun mutu

Sama da mutum 20,000 ne ake fargabar cewa sun mutu a ambaliyar ruwan Libya, a cewar wani jami’in gwamnatin yanki.

 

Bala’in ambaliyar ruwan ya shafe gabashin ƙasar ranar Lahadi.

 

Magajin birnin Derna na gaɓar teku ya faɗa wa tashar talbijin ta Saudiyya mai suna Al Arabiya cewa ya yi ƙiyasi kimanin mutum 18,000 zuwa 20,000 ne suka mutu lokacin da madatsun ruwan birnin suka fashe, inda ambaliyar ruwan tsunami ta yi awon gaba da mutane a lokacin da suke gida suna barci.

 

Alƙaluman da ya bayar sun dogara ne a kan adadin unwagunnin da ambaliyar ta ɗaiɗaita, kamar yadda ya faɗa wa gidan talbijin ɗin.

 

Gawawwakin da ba a kai ga ganowa ba har yanzu na ƙarƙashin ɓaraguzai ko kuma can a cikin teku, lamarin da ke ƙara kasadar ɓarkewar cutuka.