Sojojin Nijar 17 sun hallaka a sakamakon harin ta’addanci
Ma’aikatar tsaron jamhuriyar Nijar ta sanar da mutuwar sojojin kasar 17, a wani harin kwanton bauna da aka kai musu cikin wani yanki dake arewa maso yammacin kasar, gab da iyakar Burkina Faso.
Ta cikin wata sanarwa da ma’aikatar Sojojin Nijar da tsaron kasar ta fitar yau ta ce maharan da ake zargin yan kungiyoyin da ke ikirarin jihadi ne, sun Farmaki sojojin a sansanin su da ke kauyen Torodi, lokacin da suke bakin aiki.
Sanarwar ta kuma tabbatar cewa yayin bata kashin, sojojin sun yi nasarar hallaka ‘yan ta’adda da dama Wanda ba’a kaiga gano adadin zuwa lokacin da mukayi wannan Rahoto ba, bayan da aka kaiwa sojojin da ke wajen daukin gaggawa, amma dai duk da haka an rasa sojoji Sama da 17 a majiyar.
Tun shekarar 2021, harin ta’addanci ke zama babban kalubalen tsaro da Jamhuriyar Nijar ke fama da shi musamman a kan iyakokin kasar da Mali da kuma Burkina Faso.
Haka abin yake a kasashen na Mali da Buknina Faso da ke fama da ayyukan kungiyoyi masu ikirarin Jihadin, abinda wasu masu sharhi ke ganin lamarin na karuwa cikin hanzari tun bayan da kasashen biyu suka sallami sojojin Faransa dake tayasu yakin ta hanyar manyan makamai da Jirgin yaki bayan juyin mulki da akayi a dukka kasashen.