Labarai
Mayakan ISWAP na kwarara daga Sahel zuwa tafkin Chadi da Najeriya
Rahotanni na nuna cewa mayakan kungiyar ISWAP na barin sansanonin su dake yankin Sahel da jamhuriyar Nijar, inda suke komawa wasu sassan yankin tafkin Chadi da arewa maso yammaccin Najeriya.
kuma sun yada zango ne a jihohin Katsina, Kaduna Zamfara da Sokoto dukkanin su da ke arewacin Najeriya kusa da Nijer.
Jaridar Daily Trust a Nigeria ta ruwaito cewa tuni wannan ya fara barzana ga zaman lafiyar da aka fara samu a kewayen yankin tafkin Chadi, sai dai kuma bayanai na cewa tuni dakarun Civilian JTF Wanda sukayi tasiri wajen yakan Yan ta’addan suka fara gyara dammarar su.
Cikin wadanda ake zargin sun yi Hijirar daga yankin Sahil Wato Saharar ta Jamhuriyar Nijar zuwa yankin tafkin Chadi har da Abubakar Modu, Sheikh Ba’ana Dujum, Marte Alwady, Muhammed Ibn Abubakar da kuma El-Mansur Dawahli Mouda dukkanin su manyan kwamandoji a kungiyar ta ISWAP da keda Alaka da IS ta Duniya.