Labarai

Gwamnan Zamfara na zargin Gwamnatin Tarraya da ƙoƙarin hada kai da Yan bindiga domin sulhu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bukaci gwamnatin tarayya ta gudanar da cikakken bincike game da wata tattaunawar sulhu a boye da ake yi da Yan bindiga a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewar tawagar wasu hukumomi da Gwamnatin Tarayya ta aika sun fara tattaunawa da kungiyoyi Yan bindiga ba tare da sanin gwamnatin jihar ba.

APPLY NOW!  Sojojin Najeriya sun binne gawarwakin dakaru 20 da aka kashe

A ranar Litinin Kakakin gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar da wata sanarwa, ta nuna rashin jin dadin yadda wasu hukumomin Gwamnatin Tarayya suka gana da ƴan bindiga ba tare da tuntuɓar gwamnati da hukumonin tsaron jihar ba.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewar: ”Gwamna Dauda Lawal ya buƙaci gwamnatin tarayya ta fayyace wannan mataki na wasu hukumominta, wanda ya ci karo da ƙudurin gwamnatin jihar na amfani da ƙarfi kan Yan bindigar.

APPLY NOW!  Yan sanda sun kama wani mutum bisa laifin dukan ƴaƴansa har suka mutu

Ya ƙara da cewa ya kamata gwamnati ta binciki wannan lamari, wanda tamkar zagon ƙasa ne ga yunƙurin gwamnatin jihar na yakar Yan fashin daji.

Gwamnatin Zamfara ta ce ta samu rahoton yadda jami’an gwamnatin tarayya suka gana da ƙungiyoyin Yan fashin daji a yankunan Birnin Magaji da Maradun da Mun haye da Bawo da kuma Bagege.

APPLY NOW!  Rashin hadin kan gwamnatoci dama ce ga Yan Bindiga

“Yunƙurin yin sulhun da Yan fashi da tsohuwar gamnatin jihar ta yi a baya bai yi tasiri ba. Ya kamata mu ɗauki darasi daga kura-kuran baya tare da ɗaukar sabbin hanyoyin dawo da zaman lafiya Zamfara.”

“Kasancewar yaƙi da fashin daji na cikin manyan ƙudurorin gwamnatin jihar Zamfara, ba za mu lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga hakan ba.”

APPLY NOW!  Tirkashe Kotun Birtaniya Ta Tuhumi Diezani Kan Zargin Karbar Cin Hanci

Muna buƙatar Gwamnatin Tarayya ta ɗauki mataki nan take ta hanyar dakatar da duk wata tattaunawa da ake yi da ƴan fashin daji a Zamfara, domin hakan zagon ƙasa ne ga matakan da ake ɗauka.” In ji sanarwar.