Labarai

Majalisar Dattawan Najeriya ta tantance ministoci 14 cikin 28

Shugaban kasar Bola Tinubu ya aika mata, ciki har da tsohon Gwamnan Jihar Ribas Nyesome Wike

Majalisar Dattawan Najeriya ta tantance ministoci 14 cikin 28 da Shugaban kasar Bola Tinubu ya aika mata, ciki har da tsohon Gwamnan Jihar Ribas Nyesome Wike. To sai dai ‘yan siyasa da masana harkokin shar’ia sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan cancantar ministocin.

ABUJA, NIGERIA —

Tsohon Gwamnan Jihar Ribas Nyesome Wike wanda yana daya daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar adawa wadanda Tinubu ya zabo domin ba su kujerar Minista ya sha alwashin zai baiwa marada kunya idan ya fara aiki a matsayin Minista a Gwamnatin Tinubu.

To sai dai Sanata Sahabi Ya’u, daga Jihar Zamfara, ya ce majalisar ta tantance Ministoci 14 a maimakon 16 da Majalisar ta yi niyan tantancewa.

Sahabi ya tabbatar da cewa shugaban kasa ya zabi wadanda ya ke ganin sun cancanta wajen yi wa kasa aiki musamman ma ta bangaren hada kan kasa.

Sahabi ya ce talakan da ke Najeriya ya dauki Tinubu a matsayin wani wanda zai share masu hawaye wajen fidda Najeriya halin da ta ke ciki.

Ya ce Shugaba Tinubu yayi kokarin nuna cewa shi mai bin doka ne wajen kawo sunayen ministoci a cikin watani biyu na mulkin sa kamar yadda doka ta tanada kuma wannan abin yabawa ne.

Amma ga masanin shari’a Barista Mainasara Kogo Ibrahim Umar, yana ganin akwai abin dubawa a wadannan Ministocin da Tinubu ya zakulo saboda kawo tsofaffin Gwamnoni ko tsofaffin Ministoci ko wadanda suka rike mukamai da dama a baya, yana nuni da cewa kasa ba za ta ci gaba a haka ba, idan ana maimaita mutane iri daya a mukamai akai-akai.

Mainasara ya ce abin da ya dace shi ne, a ba da dama wasu masu sabbin tunani da sabbin kwakwalwa su shigo cikin harkar gudanarwa domin su kawo sauyi .

Ya kara da cewa “mafi rinjayen wadanda aka ba su mukaman minista su 28 din nan, su ne unguwan zomar mafi yawancin matsalolin da kasar ke ciki. Wannan zubi ba zai banbanta da irin tsarin da aka yi a Gwamnatin da ta shude ba.”

To ko minene doka ta tanada kan batun nada Ministoci, ganin cewa wasu jihohi sun samu ministoci bi-biyu amma wasu ba a riga an ba su ba?

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Soma Tantance Ministoci

Majalisar Dattawa

Sanata Babangida Husseini ya yi karin haske cewa abin da doka ta tanada shi ne kowace jiha ya kamata a ba ta minista daya, kuma nan gaba shugaban zai aiko da sauran sunayen.

Babangida yace “bayan jiha an amincewa shugaban kasa ya dauko daga shiya ya nada minista, shi ya sa ake samun ministoci fiye da 36 ko 37 idan an hada har da Birnin Tarayya. Wani zubin ma sai a sami 40 ko fiye da haka.”

Ana sa ran tantance sauran ministoci 14 nan ba da jimawa ba.