Gobara ta hallaka sama da mutum 60 a Afirka Ta Kudu
Gobara ta hallaka sama da mutum 60 a Afirka Ta Kudu
Ma’aikatan agajin gaggawa da ‘yan kwana-kwana a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu, sun ce sama da mutane 60 sun mutu sakamakon gobara da ta tashi a wani rukunin gidaje.
Jami’an sun ce mutane da dama sun ji mummunan rauni, kuma hukumomi sun ce ba a kai ga gane musabbabin tashin gobarar a ginin mai hawa biyar da ke wata unguwa a tsakiyar birnin ba.
Mai magana da yawun hukumar gaggawa Robert Mulaudzi ya shaidawa BBC ‘yan kwana-kwana sun yi nasarar fito da wasu mutane daga ginin.
Ya kuma ce wutar ta mamaye daukacin ginin, hakan ya zama abu mai matukar wuya ga ma’aikatansu, amma duk da hakan za a ci gaba da neman wadanda watakil suka maƙale a ginin.
Kawo yanzu dai an kai ga gano kimanin gawarwakin mutane 73 da suka mutu da kuma wasu 43 suka samu munanan raunuka sakamakon gobarar da tatashi a ƙasar Afirka ta Kudu.
Jami’in hukumar da ke bayar da agajin gaggawa na kasar, Robert Mulaudzi, ya shaidawa wata kafar watsa labaran ƙasar ta ENCA, cewa akwai fargabar adadin na iya ƙaruwa.
“Muna bi ɗaki-ɗaki domin gano waɗannan gawarwaki.” in ji shi.
Amma a wani rahoton da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Johannesburg ta fitar ya bayyana cewa yawan waɗanda suka mutu ya kai mutum 73.
Kazalika ana kan ci gaba da gudanar da aikin neman waɗansu da ake kyautata zaton sun hallaka.
Wasu rahotanni na cewa galibin mutanen da ke cikin ginin da gobarar ta rutsa da su baƙin haure ne, da kuma ke zaune a ginin ba bisa ƙa’ida ba.
‘Yan Afirka ta Kudu da dama ne ke Alla-wadai da kalaman wariya da wasu ‘yan ƙasar ke yi a shafukan sada zumunta inda suke famar sukar waɗanda gobarar ta rutsa da su.