Labarai

Wace illa juyin mulkin Nijar zai yi wa duniya?

Waɗanda aka ɗorawa alhakin tsaron Zaɓaɓben Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum su suka hamɓarar da gwamnatinsa.

Shugaba Bazoum ya kasance na farko da ya gaji shugaban da wa’adin mulkinsa ya kammala karon farko tun bayan da Nijar ta samu ƴanci a shekara ta 1960.

Nijar na a wani muhimmin yanki ne a Afirka da aka fi sani da Sahel wanda ya ke fama da ayyukan masu ikirarin jihadi, kuma yanki ne da gwamnatocin sojoji suka kewaye shi.

Mene ne ya sa Nijar ke da muhimmanci?

A matsayinta ta ƙasa mafi faɗin ƙasa a Afirka ta Yamma kuma mahaɗar hanyoyin ƙasashe ce.

Kasashen Faransa da Amurka sun haɗa gwiwa da ita wajen yaƙar masu ikirarin jihadi.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayyana Nijar a matsayin abokiyar yaƙi da ta’addanci kan ƙungiyoyin Islama daban-daban masu alaƙa da IS da kuma Al-Qaeda.

Sai dai duk da haka ana kallon al`ummar ƙasar a matsayin matalauta.