Labarai

Anfani da fetur a Najeriya ya ragu kashi 35 cikin 100

Hukumar kula da harkokin da sarrafawan tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, NMDPRA ta ce yawan man fetur da ake amfani da shi a ƙasar a kowacce rana ya ragu zuwa lita miliyan 46.34, sabanin 65M sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.

 

Shugaban hukumar, Ahmed Farouk, ne ya bayyana haka a lokacin taron manyan masu ruwa da tsaki kan harkokin albarkatun man fetur da iskar gas a birnin Legas, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN ya ruwaito.

APPLY NOW!  Yadda zai faru idan aka kwace kujeran Gwamna a Kotun Gaba

 

Ya ƙara da cewa raguwar ta kai kashi 35 cikin 100 idan aka kwatanta da lita miliyan 65 Asalin da ake amfani da shi a kowacce rana kafin cire tallafin man fetur ɗin.

 

Ahmed Farouk ya ce ”a watan Janairu fabrairu, an sha mai lita miliyan 62 a kowacce rana, yayin da aka sha lita miliyan 71.4 a kowace rana cikin watan Maris, sai Afiru da aka sha lita miliyan 67.7 a kowacce rana, sai watan Mayu da aka sha lita miliyan 49.5 a kowace rana, sai kuma watan Yuli da ake shan lita miliyan 46.3 a kowace rana”.

APPLY NOW!  Ta yaya zan kare kaina daga ciwon hanta?

 

Shugaban hukumar ya kuma gode wa ‘yan kasuwar da suka nuna sha’awarsu wajen shigar da man fetur ƙasar daga kasuwannin duniya.

 

Ya kara da cewa kawo yanzu kamfanoni 56 ne suka nuna sha’awarsu wajen shigo da man fetr zuwa ƙasar, yayin da kamfanoni 10 suka zaku wajen fara shigo da man.

APPLY NOW!  A karon farkon tawagar ECOWAS ta gana da Bazoum

 

Ahmed Farouk ya ce yanzu haka kamfanoni uku sun fara shigo da man fetur ɗin daga ƙasashen waje.