Labarai

Rasha za ta kammala samar wa Najeriya jiragen yaki

Rasha na shirin kammala samar da jiragen yaki masu saukar ungulu na Mi-35 guda 12 ga Najeriya, kamar yadda wani jami’i ya shaida wa kamfanin dillancin labaran ƙasar, Rian, a wajen taron Rasha da Afirka da ke gudana a Rasha.

Dmitry Shugaev, shugaban ma’aikatar tarayya ta Rasha kan fasahar aikin soji da tsaro, ya ce yarjejeniyar sojan ita ce ta taimaka wa Najeriya wajen yaƙi da barazanar kungiyoyin ƴan ta’adda da kuma shigar da ƙasar cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Bai bayyana adadin jiragen yaƙin da aka kawo ba zuwa yanzu ko kuma lokacin da za a kammala kawo sauran jiragen ba, amma ya ce “Ƙasashen na sha’awar kammala jigilar jiragen, muna ci gaba da yin aiki ta wannan fuskar.”

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya ce Najeriya za ta haɗa gwiwa da ƙasar Rasha domin farfaɗo da kamfanin sarrafa aluminium.

Yarjejeniyar dai na daga cikin yarjejeniyoyin da ake sa ran za a ƙulla a yayin taron, wanda shi ne irinsa na biyu bayan da aka yi na farko a shekarar 2019 a birnin Sochi.

APPLY NOW!  Farashin dala na ci gaba da sauka a Najeriya

Mista Kashim Shettima dai yana halartar taron ne tare da wasu shugabannin ƙasashen Afirka.

Tuni dai Rasha ta yi alkawarin samar da hatsi kyauta ga Zimbabwe da wasu ƙasashen Afrika biyar.