Labarai

Shugaban ECOWAS bola Tinubu ya sakawa Nijar Dokoki

Shugaban ECOWAS bola Tinubu ya sakawa Nijar Dokoki Akan juyin mulki

Gaskiya ina fahimtar akwai gyara ko kuskure a matakan da ECOWAS ta ‘dauka akan lamarin juyin Mulkin kasar Nijar. ‘Kungigar hadin kan cigaban kasashen Africa ta Yamma (ECOWAS) ko CEDEAO da Faransanci, wanda shugaba Tinubu na Nigeria yake shugabanta, abinda nake fahimta shine:

 

1. Kuskure ne a lokaci guda ECOWAS ta saka Economic Sanctions wa kasar Nijar, wato Takunkumin tattalin arziki akan Kudade, Abinci da sauran harkokin kasuwanci da zirga zirgan jiragen sama.

~ Domin talakawa abun zai illata, ni nafi fahimtar ECOWAS ta dauke su gaba daya ta bar na zirga zirgan jiragen sama, da kuma Intenational Fund transfers zuwa Nijar sai dai cikin West Africa kawai. Wato a dakatar da hada hadar tura Kudade zuwa kasashen da ba Africa ta Yamma ba.

 

2. Na biyu, shugaba Tinubu da yake jagorantar ECOWAS ba Soja bane, kada wajen kokarin yin jarumta ka jefa Miliyoyin mutanen da ba ‘yan kasar ka ba cikin damuwa, domin kwanaki 7 da kace ECOWAS ta baiwa Sojoji su sauka su dawo da Muhammad Bazoum kan Mulki yayi kadan, domin (Transition) ko mika Mulki a Dimokradiyyance ma yana tayar da Kura balle a mulkin Soja. Mulkin da aka karba da karfi bala’i da Bakin Wuta da Bindiga.

APPLY NOW!  Gwamnatin Najeriya tayi bayani akan shiri na sake dawo da tallafin mai

 

~ Ka duba takaddamar da aka tayi tsakanin ka da tsohuwar Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria.

 

3. Abu na uku, idan ‘daukan wadannan matakan dai dai ne me yasa ECOWAS bata dauki irin su ba akan kasar Mali, Burkina Faso, Guinea, wadanda suma duk anyi juyin Mulki a baya bayan nan ‘kasa da shekaru uku da suka gabata?

~ Karfin Soja da kuka ce za kuyi amfani dashi ba zai taba kawo mafita ba, duba tarihin Yakin Rasha da tsohuwar tarayyar Soviet (Soviet Union) data rushe a 1991, amfani da Bakin Wuta ba zai magance matsalar ba sai dai a kashe wadanda basu ji basu gani ba.

 

~ Ka duba yadda America ta shiga Iraq a 2003 duk da cewa ta samu goyon bayan ‘yan Shi’a ‘yan Northern Alliance, karshe da kafan su suka gudu suka bar kasar, Barack Hussaini Obama shi ya fara tattaro Sojojin su daga can suka fara dawowa gida.

APPLY NOW!  An Kuma: Sojojin Gabon sun ce sun yi juyin mulki

~ Trump da Biden suka zo suka kammala.

Amma daga karshe me suka ce? shine sun kashe Kudade, sun bata shekaru kusan 20, an kashe musu Sojoji da jama’an su. Kuma manufar su bata samu ba.

 

Just of recent, ka duba Rasha ta shiga Ukraine da Sojojin ta, da Kudaden ta, da karfin ta, yau kusan shekaru biyu har yanzu Rasha bata samu abinda take so na nasara ba. Wannan shine abinda amfani da karfin Soja yake jawowa.

~ Duk yadda America take Neman Osama Bin Laden, Aiman Al-Zawahiri, Mullah Muhammad Umar daga karshe sai data ajiye Sojojin ta, ta shigo kasuwa ta zuba Kudi cewa duk wanda ya kawo mata su ga Kudi Dala kaza da kaza. Jiragen Anaconda da America ta ‘kera masu Siffar Maciji don su yaki ‘yan Taliban a cikin Duwatsun kasar Pakistan, Afghanistan, Iraq da sauran su ba suyi amfani ba.

 

4. Na Hudu, wannan Yakin da ECOWAS take cewa za’a iya bugawa da Sojojin da suka kifar da gwamnatin Bazoum, kudaden kasashen Africa ta Yamma za’a tattara aje yi wannan Yakin fa? Gashi Rasha zata shigo ta taimaki Sojojin da suke mulkin Nijar din.

APPLY NOW!  Abin da ya kamata ku ci idan kuna son yin ƙiba

~ Idan ba bala’i ake son jawo mana ba a zauna dasu akan Tebur mana.

 

Ku kuma ‘yan uwan mu jama’an kasar Nijar kuyi hakuri kada ku bari wani yasa ku fito zanga zanga, kada ku goyi bayan zanga zanga, kaso 90 din ku kun yarda da Al-Qur’ani, ku karanta kuyi Tawassuli dashi, shine kawai abinda za kuyi Allah ya saurare ku, amma ECOWAS ina zargin babu wani matakin azo a gani idan ba na siyasa ba da zata dauka akan kasar ku.

 

~ Idan zanga zanga ne kuke tunanin mafita, ku duba kasar Tunisia a 2012, yau Ina take?

Duka kasar Masar a 2013.

Duka Liberia.

Kalli Sudan ta Kudu, kasar shugaba Salvakier.

Kalli Libya ta shugaba Gaddafi.

Yanzu an nufo Nijar, kuyi a hankali.

 

Muna tare daku muna muku addu’ar alkhairi kamar yadda kuke yi mana.

 

Allah yasa mu dace…..

✍️:

Abdul-Hadee Isah Ibraheem.