Labarai
Gwamnatin Osun ta soke bikin samun Yancin kan Najeriya
Babu wani Yan'ci a kasarda Baka ISA kayi tafiyar Kilometers 50 babu tashin hankali ba
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya soke bikin samun ƴancin kan Najeriya a faɗin jihar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Olawale Rasheed, ya fitar, ta ce, gwamna Adeleke ya buƙaci ƴan jihar ta Osun da su yi amfani da lokacin wajen yi wa Najeriya addu’ar samun zaman lafiya.
“Mu yi amfani da ranar bikin samun ƴancin kai wajen yi wa jihar mu da kuma ƙasa addu’a. Mutane na cikin mawuyacin hali. Lokaci ya yi da za mu roki Allah wajen samun sauki a harkokinmu,” in ji gwamna Adeleke.
A ranar Lahadi 1 ga watan Oktoban 2023 ne aka shirya gudanar da bikin na bana, domin murnar cikar Najeriya shekara 63 da samun ƴancin kai daga Turawa mulkin mallaka na Birtaniya.