Labarai

Shugaba Biden na fuskantar barazanar tsigewa

Shugaba Biden na fuskantar barazanar tsigewa

Shugaba Biden na fuskantar barazanar tsigewa

29 Satumba 2023, 04:09 GMT

Wanda aka sabunta Sa’o’i 2 da suka wuce

Ƴan majalisar wakilan Amurka na jam’iyyar Republican sun bayyana ranarsu ta farko ta kaddamar da bincike kan Shugaban ƙasar Joe Biden a matsayin nasara.

 

Sai dai biyu daga cikin ƙwararrunsu masu bayar da sheda sun ce zuwa yanzu babu isasshiyar shedar da za ta tallafa wajen tsigewar.

APPLY NOW!  Anfani da fetur a Najeriya ya ragu kashi 35 cikin 100

 

Harkokin kasuwanci na ɗan shugaban ƙasar Hunter su ne suka mamaye zaman da majalisar ta yi a ranar Alhamis na tattauna batun shirin tsigewar.

 

Ƴan majalisar na jam’iyyar Republican sun yi zargin cewa Shugaba Biden ya amfana da harkokin kasuwancin dan nasa.

Ƴan majalisar na Republican sun yi shekaru suna gudanar da bincike a kan ɗan shugaban kamar yadda ma’aikatar shari’a ta Amurka ita ma take yi.

Duka wannan na kasancewa ne yayin da shi ma Shugaba Biden ya caccaki tsohon shugaban ƙasar Donald Trump inda ya bayyana shi a matsayin barazana ga dumukuraɗiyyar Amurka.

Biden ya ce ƙoƙarin Trump na neman sake samun shugabancin ƙasar na cike ne tattare ne da neman ramuwar gayya

Mista Biden ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar wajen taron tunawa da marigayin dan majalisar dattawa na jam’iyyar Republican, John McCain, a Arizona.

APPLY NOW!  Ambaliya ta kashe mutane a Kebbi

Ya ce jam’iyyar Republican duk da cewa ba dukkanin mabiyanta ba ne ke bin aƙidar Trump ɗin to amma a yanzu masu tsattsauran ra’ayi ne ke tafiyar da ita.

Shugaban ya zargi Trump da magoya bayansa da yada aƙidoji na ƙarya da neman haddasa husuma.

Duk da cewa sai nan da shekara ɗaya da ƴan watanni za a yi zaɓen shugaban ƙasar na gaba to amma sakamakon ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a ya nuna za a yi kusan kan-kan-kan idan Trump ya samu tikitin yi wa Republican takara.

APPLY NOW!  An Kuma: Sojojin Gabon sun ce sun yi juyin mulki

Shugaba Biden na fuskantar barazanar tsigewa » Alfijir