Labarai

Rashin hadin kan gwamnatoci dama ce ga Yan Bindiga

Masana kan al’amuran tsaro sun yi gargadin cewa rashin hadin Kan Gomnatoci aiki tare tsakanin hukumomin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi kan kokarin samar da tsaro a yankin Arewa maso Yamma, zai mayar da hannun agogo baya, sannan ya bai wa yan bindiga damar cin karensu ba babbaka.

Masanan suna mayar da martani ne kan korafin da gwamnatin jihar Zamfara ta yi cewa wasu hukumomin gwamtin tarayyar kasar suna tattaunawa da ‘yan bindiga ba tare da sanin gwamnatin jihar ba, tana mai neman a gudanar da bincike kan lamarin.

A cewar masana fannin tsaro, fitowa fili gaba-gaɗi da Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi ta na ƙorafi, kan yunƙurin da wasu hukumomin gwamnatin tarayya ke yi na tattaunawar sulhu da yan bindigar, ya nuna wagegiyar ɓarakar da ake da ita tsakanin ɓangarorin biyu.

Dr Kabiru Adamu, wani mai sharhi kan lamuran tsaro a Najeriya a Najeriya, ya ce kundin ƙasar ya fayyace ayyukan ko wanne ɓangare tsakanin ɓangarorin biyu a fili.

See Also  Wani ɗan ƙaramin jirgi mai saukar angulu ya yi haɗari a Legas

A tattaunawarsa da BBC Dr Kabiru ya ce “tsaro hurumi ne na gwamnatin tarayya amma aiwatar da shi a jiha yana buƙatar haɗin kan gwamnatin jihar.

“Akwai majalisar tsaro a kowacce jiha, wadda kuma gwamnan wannan jihar shi ke shugabantarta, babu yadda za a yi a shiga jiha aiwatar da tsaro ba tare da sanin wannan majalisar ba, kuskure ne,” in ji Dr Kabiru.

Ya ƙara da cewa duk tsarin da gwamnatin tarayya ta fito da shi ba za ta taɓa cimma shi ba, ba tare da haɗin kan gwamnatin jiha ba.

“Duk lokacin da siyasa ta shiga harkokin tsaro, ya kuma zama an samu rabuwar kai tsakanin gwamnatin tarayya da ta jiha to babu wanda zai amfana da hakan sai ‘yan bindiga, domin kuma da ɓarakar da ke tsakani za su kassara ɓangarorin biyu,” in ji Dr Kabiru.

Group Captain Sadiq shi ma wani masanin tsaro ne a Najeriya ya ce haɗin kan bangarorin tarayya da gwamnatin jiha ne zai kai su ga murƙushe ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane.

See Also  Abu uku da manyan hafsoshin tsaron ECOWAS za su mayar da hankali

“Abin da ya sa ba a samun nasara a wannan yaƙin tun da daɗewa shi ne yadda hukumomi da gwamnatoci ke aiki ba tare ba.

“Bai kamata a ce an shiga cikin jihar gwamna ba, bai sani ba. Ya fi kowa kusa da mutanensa kuma shi ne yake da cikakkun bayanai sama da wanda duk za a tura daga Abuja domin kai ɗauki,” in ji Group Captain.

Masanan sun ce bai kamata a fara sulhu da ‘yan bingida ba tare da sanin gwamnatin da take shugabantar jihar ba.

Dr Kabiru ya ce kuskuren da gwamnatin jihar Zamfara ta yi shi ne yayata wannan ƙorafi nata a kafafen ‘yaɗa labarai, maimakon ta tunkari gwamnatin tarayya domin su tattauna.

Shi kuma Group Captain Sadiq cewa ya yi wannan ne karon farko da ake ganin haka a fannin yaƙi da ‘yan bindiga da ake yi, lokaci bai ƙure ba na shawo kan matsalar ta zama an ɗinke ta tamkar ba ta taba faruwa ba.

See Also  Najeriya da Kanada za su hada kai don