Labarai

Sojojin Najeriya sun binne gawarwakin dakaru 20 da aka kashe

Rundunar sojin Najeriya ta binne gawarwarkin dakarunta 20 da ‘yan bindiga suka yiwa kwanton-ɓauna suka kashesu a Nijer State.

A makon da ya gabata sojojin suka ce dakarunsu 36 aka kashe a wani kwanton-ɓauna da ‘yan ta’adda suka yi musu a kan hanyar Zungeru zuwa Tegina, sannan kuma da faduwar wani jirgin yaƙin sojin a yankin Chukuba da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja Wanda yaje dauko Sojojin da sukaji Rauni.

Rahotonni sun ce jana’izar ta samu halartar ministocin tsaron kasar biyu Muhammad Badaru Abubakar da Bello Matawalle, tare da babban hafsan tsaron ƙasar Janar Christopher Musa Active.

Sauran manyan baƙin da suka halarci jana’izar sun haɗar da babban hafsan sojin ƙasa Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, da babban hafsan sojin ruwa na ƙasar da sauran iyalan gwarazan dakarun da Nijeriya din da suka Mutu.

Buhari ya jajanta wa iyalan sojojin Najeriya da aka kashe a Neja

Sojojin Najeriya sun yi wa ɗan fashi Alhaji Shanono da yaransa 17 ruwan wuta a Kaduna

APPLY NOW!  DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnati ta hana sayar da finafinai fassarar Indiya