An Kama Wasu Mata Guda biyu Da Harsasin Bindiga
An Kama Wasu Mata Guda biyu Da Harsasin Bindiga
AN SAN IYAYE MATA DA TAUSAYI
Ba shakka an san iyaye mata da tausayi da jin-kai, sai dai kash ba haka abin yake ba a gurin wadannan matan aure guda biyu Rashida Umar da Rukaiya Ladan
Jami’an ‘Yan sandan sirri sun kama Rashida da Rukaiya a garin Akwanga dake jihar Nasarawa dauke da harsashin bindiga sama da guda dubu daya
Wadannan matan sun dauko harsashin ne daga wani gari da ake kira Fadan-Karshe dake karamar hukumar Sanga na jihar Kaduna zasu kaiwa ‘yan ta’addan jeji a Kontagora na jihar Niger
A tunaninku wani irin kuncin rayuwa ne zai sa wadannan mata shiga wannan mummunan harka na safaran makamai zuwa ga ‘yan ta’adda?
Talauci?
Yunwa?
Rashin samun kula daga mazajensu?
Rashin tsoron Allah?
Yanzu me zasu fadawa mazansu na aure da ‘ya’yansu da iyaye da ‘yan uwansu? Abin akwai tausayi da bacin rai
Allah Ya sauwake