Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Wa Dakarun Ta Kashedi
Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Wa Dakarun Ta Kashedi
Rundunar Sojin Najeriya ta yi wa dakarunta kashedi dangane da takon-saka da ke wanzuwa tsakanin gwamnatin Sojin Jamhuriyar Nijar da kungiyar ECOWAS.

KAI-TSAYE
Search
NAJERIYA
Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Wa Dakarun Ta Kashedi Kada Su Dauki Umurnin Da Ba Ita Ta Bayar Ba
4 hours ago
Muhammadu Nasir Hadiza Kyari

Rundunar sojin Najeriya

Dubi ra’ayoyi
Rundunar Sojin Najeriya ta yi wa dakarunta kashedi dangane da takon-saka da ke wanzuwa tsakanin gwamnatin Sojin Jamhuriyar Nijar da kungiyar ECOWAS.
SOKOTO, NIGERIA —
Wannan na zuwa ne lokacin da labaran kanzon kurege ke yawo barkatai a shafukan Sada zumunta na yanar gizo, akan rikicin.
Takun-saka da ke wanzuwa tsakanin Jagororin Gwamnatin Soji da ta yi juyin mulki a Jamhuriyar da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta ECOWAS, na ci gaba da sa fargaba da rashin tabbas tsakanin mutanen kasashen biyu musamman a jihohin da kasashen ke makwabtaka da juna.
A wata ziyara da babban hafsan mayakan kasa na Najeriya Lt. Janar Taoreed Lagbaja ya kai a jihar Sakkwato wadda tana daya daga jihohin da ke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar, ya yi gargadi ga dakarun soji da ke yankin runduna ta takwas da cewa, koda yaushe su kasance cikin shirin ko-ta-kwana, amma kuma su kasance masu karbar umurni daga rundunar tsaron Najeriya.
Yace dukan sojin suna da masaniya a kan abin da ke gudana a Jamhuriyar Nijar da kuma yadda zai iya shafar Najeriya.
Ya kara da cewa ya tabbata da yawan sojin suna amfani da kafar sada zumunta ta yanar gizo, suna ganin batutuwan da ke yawo.
“Mutane na yada jita-jita, suna kokarin ingiza Rundunar Soji shiga sharu ba shanu, to kasancewar su kwararrin jami’an soji masu da’a dole ne su kauda ido daga bin ra’ayin siyasa.
Dole ne su kasance masu biyayya ga gwamnati da kundin tsarin mulki, kar su karkata kan abinda ke yawo a yanar gizo, domin masu yada bayanai suna yi ne bisa wata manufa da suke da ita.”
Ya sheda musu cewa, gwamnatin Najeriya ce zata dauki matsaya a kan batun, kuma matsaya mafi dacewa ga kasa.
Tun lokacin takaddamar ta soma yin zafi ne ake ta ganin bayanai har ma da hotuna a shafukan sada zumunta na yanar gizo, wadanda ba lallai na gaskiya ne ba, duk da yake da yawan al’ummomin kasashen biyu fatar su a warware takaddamar cikin ruwan sanyi.
Har yanzu dai jama’ar kasashen biyu na ci gaba da fuskantar damuwa da matsanancin yanayi da matsalar ta haifar.