Yan Boko haram kusan 100 sun mutu a fadan Suyasu
Bayanai daga jihar Borno da ke arewacin Najeriya na cewa mayakan Boko Haram 82 sun rasa rayukansu a wani rikicin kabilanci da suka yi a tsakaninsu.
Rahotanni sun ce, mayakan na Boko Haram sun gwabza da juna a cikin Karamar Hukumar Kukawa ta jihar Borno.
Jami’an tsaro da ke aikin sa-kai a yankin tafkin Chadi JTF da Baga sun shaida wa manema labarai cewa, mayakan kusan 100 sun mutu, yayin da wasu kuma da dama sun jikkata.
Wasu majiyoyi sun shaida wa Jaridar cewa, fadan ya samo asali ne bayan da wasu ‘yan Boko Haram ‘yan wata kabila daban suka kashe ‘yan uwansu ‘yan Boko Haram amma ‘yan kabilar Buduma.
Majiyar ta kuma ce, kwamandan tsagin da suka yi kisan ne ya bude musu wuta, bayan da ya sami labarin cewa suna shirin mika wuya ga rundunar sojin Najeriya.
Tun farko dai an gano cewa sun shaida wa wasu abokansu cewa su fa, sun gaji da aikin ta’addanci suna shirin mika wuya ga rundunar sojin Najeriya, su kuma suka ci amanarsu ta hanyar gaya wa kwamandansu, ba kuma tare da bata lokaci ba ya gayyace su sansaninsa da ke yankin Bukkuwaram, bayan kwarya-kwaryar shari’a ne kuma ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar harbi.
Bayan wannan kisa ne kuma tsagin Boko Haram din da wadanda aka kashe suka fito, ke ganin kawai ya kashe su ne don ba ‘yan kabilarsa ba ne, don kuwa a baya akwai ‘yan kabilarsa da suka mika wuya kuma bai yi musu komai ba.
Wasu hujjoji sun ce, wannan fadan ba shi da wata nasaba da ta’addanci, fada ne kawai na kabilanci a cikin kungiyar ‘yan ta’addar Boko Haram.
Wannan fada ya tilasta wa wasu daga cikin ‘yan ta’addar tserewa zuwa wasu sassan jihar Borno da kuma kananan kauyuka da ke iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.