Labarai

Wani baturen Birtaniya yayi lalata da karnuka

Wani baturen Birtaniya yayi lalata da karnuka

Wani sanannen mai nazari kan rayuwar kadoji ɗan asalin Birtaniya ya amsa tuhumar da ake yi masa ta yin lalata da dabbobi da kuma mallakar abubuwan da suka jiɓanci cin zarafin yara.

 

Wata kotu a ƙasar Australiya ce ta saurari ƙarar, kan cewa Adam Britton ya ɗauki bidiyon kansa yana azabtar da gwamman karnuka har kusan dukkanin su suka mutu.

APPLY NOW!  NDLEA ta kama dala miliyan 20 da take zargin na boge ne

 

Haka nan mutumin ya riƙa wallafa irin waɗannan bidiyoyi a shafukan intanet.

 

Yanzu haka dai ana jiran kotu ta ajiye ranar da za ta yanke hukunci a kan mutumin, wanda ya taɓa yin aiki da BBC da kuma tashar talabijin mai shirye-shirye kan rayuwar dabbobi ta National Geographic.

 

A lokacin sauraron ƙarar a ranar Litinin, alƙalin kotun ya ce yawancin bidiyon da aka kawo a matsayin shaida sun yi muni da yawa, inda aka gargaɗi mahalarta kotun kan cewa za su iya fita domin gudun kada hankulansu su tashi.

APPLY NOW!  Gwamnatin Najeriya Za Ta Sake Gurfanar Da Emefiele Kan Wasu Sabbin Tuhume-tuhume

 

Alƙalin kotun, mai shari’a Michael Grant ya ce ya damu kan cewa bayanan abubuwan da Britton ya aikata za su iya haifar da mummunar damuwa ga mahalarta kotun, inda ya buƙaci jami’an tsaro da ƙananan ma’aikatan kotun da su fita daga zauren.

 

Masu gabatar da ƙara sun ce Britton ya kasance mai ‘matsananciyar muguwar aniya da son yin lalata da dabbobi’ tun aƙalla shekarar 2014.

APPLY NOW!  Yan sanda sun kama wani mutum bisa laifin dukan ƴaƴansa har suka mutu

 

Sun ce baya ga cin zarafin nasa dabbobin, ya kuma shawo kan wasu mutane daban domin su ba shi ajiyar dabbobinsu, waɗanda su ma ya ci zarafin su.

 

An tabbatar da cewa ya riƙa cin zarafin dabbobin ne a wani ɗakin kwantena da ya mallaka, wanda ya maƙala wa kyamarori, kuma ya laƙaba wa wurin sunan “ɗakin azabtarwa.”

APPLY NOW!  Girgizar Kasa Ya Hallaka Dalibai A Morocco

 

An bayyana cewa daga cikin karnuka 42 da ya ci zarafi a tsawon wata 18, guda 39 sun mutu.

 

Yanzu haka dai ana tsare da Briiton tun bayan da aka kama shi, inda ake sa ran yanke masa hukunci a watan Disamba.

 

An haife shi ne a yankin West Yorkshire na Birtaniya, inda ya koma Australia shekaru 20 da suka gabata domin yin aikin da ya shafi kadoji.

APPLY NOW!  Yan Kalare Sun Cirewa Wani Hannu A Gombe
Advertisement