Labarai

CIN AMANA A YAKI DA TA’ADDANCI A NIGERIA

CIN AMANA A YAKI DA TA'ADDANCI A NIGERIA

CIN AMANA A YAKI DA TA’ADDANCI A NIGERIA

 

Wannan shine sakamakon binciken da na yi akan harbo jirgin yakin Nigeria da ‘yan ta’adda sukayi a jihar Niger tare da bada wasu shawarwari ta fuskar tsaro

 

Wannan jirgin da ‘yan ta’adda suka harbo a jihar Niger sunansa Mi17-E, jirgin yaki ne wanda Shugaba Buhari ya saya a shekarar 2021, sophisticated fighter aircraft ne, Kasar Jamus ne ta sayar wa Nigeria Jirgin, ta rage kashi 50 cikin 100 na kudin jirgin, kudin jirgin a yanzu ya kai Kimanin Naira Biliyan 18

 

‘Yan ta’addan ISWAP wanda suka hade da barayin Daji sune suka harbo jirgin suka kashe babban matukin jirgin Flight Lieutenant Ibrahim Adamu da wani Pilot da wasu Injiniyoyin jirgi mutum biyu

 

Lokacin da jirgin ya tashi zuwa dauko gawarwakin Sojoji da aka kashe a Niger sai ya zama ba’a bada umarni jirgin ya dauki makamin yaki ba, shi wannan jirgin bullet proof ne, ma’ana harsashin kowani irin bindiga ba zai iya huda jirgin ba, duk ruwan harsashin bindiga da za’a yiwa jirgin ba zai hudashi ba

APPLY NOW!  Sojojin Najeriya Sun Kai Hari Kan Rumbunan Ajiye Makaman ‘Yan Kungiyar IPOB

 

Wani zaiyi tambaya cewa ya akayi jirgin ya fado tunda baya jin harsashi ko bomb? To ga amsar tambaya

👇

Kowani irin jirgi kirar helicopter (mai saukar ungulu) yana da Propeller guda biyu, daya a sama daya a jelar jirgin, propeller dake jelar jirgin karami ne amma shine yake bawa babban propeller na sama umarni, to a propeller na jelar jirgin akwai abinda suke kira da Rotor

 

Rotor shine yake sarrafa yanayin kadawa da juyawan jirgi a sama, dazaran bullet ya taba rotor to jirgin zai rasa direction ya kauce har ma ya fado kasa, to abinda ya faru da jirgin kenan, ‘yan ta’addan da bindigar AK47 suka kado jirgin, kuma rotor na jirgin suka taba, wannan shine matsalar kowani irin jirgin mai saukar ungulu, da zaran rotor dinsa ya tabu to jirgin zai rasa direction ya fadi

 

Idan kun saurari bayanin ‘yan ta’addan a bidiyo da na saka a Telegram a wannan link https://t.me/+SdOQ7Dw3-zmK-2-C

APPLY NOW!  Menene gaskiyar labarin da ake yadawa, na farashin Man Fetur zai koma Naira 250 ko 300 a sati mai zuwa?

zaku ji ‘yan ta’addan suna cewa da normal AK47 suka harbo jirgin, kuma maganarsu gaskiya ne wannan rotor suka taba saboda jirgin baya jin bullet, shiyasa jirgin ya fadi

 

Wannan jirgi Mi17-E anyi deploying nasa a Airforce base dake Bauchi, daga baya sai Shugaba Buhari yasa aka mayar da jirgin zuwa Katsina don a yaki bandit dashi, to daga Katsina jirgin ya kan tafi Kaduna inspection, bayan zuwan jirgin Kaduna domin inspection sai ya zama jirgin yana da sauran awa daya da mintuna shabiyar (1:15) da ya rage wa jirgin ayi inspection dinsa, sai akace bari ayi amfani da sauran lokacin da ya rage wa jirgin aje a debo Sojojin da aka kashe a Zangeru jihar Niger ba tare da an daura wa jirgin makamai ba

 

Inda aka samu kuskure ko ganganci ko cin amana ko rashin sanin aiki daga wanda zai bada umarni shine, a ilmin tsaro da kuma combat operation idan an yiwa jami’an tsaro harin kwanton bauna (ambush) ba’a zuwa kai tsaye ace za’a dauko gawar wadanda aka kashe ko wadanda suka samu raunuka, saboda wadanda sukayi ambush din a farko sun san za’a zo, don haka zasu sake shirya harin kwanton bauna karo na biyu

APPLY NOW!  Farashin dala na ci gaba da sauka a Najeriya

 

Da aka tabbatar sun yiwa Sojoji ambush sun kashe su, abinda ya kamaya ayi shine, ba jirgin yaki carrier za’a fara turawa ba, jirgin yaki mai leken asiri marar matuki ya kamata a fara turawa yayi air surveillance a gurin da aka kashe sojojin, duk abinda yake gurin zai gani, idan ‘yan ta’addan suna nan daga nan sai a aika jirgin yaki dauke da makamai ya jefa musu bomb daga sama ya musu ruwan harsashi, amma ba’ayi haka ba, sai aka tura wannan wanda ko bindiga bai dauka ba, har abinda ya faru ya faru, anyi asaran rayuka na matuka jirgin yaki mutum biyu, anyi asaran jirgi mai tsadan gaske, sannan anyi asaran injiniyoyin jirgi

 

Duk kwamandan yaki da ya san aikinsa ba zai yi irin wannan ganganci ba, sai dai watakila idan yana da wata manufa na cin amanar tsaro, don haka ya cancanci a bashi query mai zafin gaske

 

APPLY NOW!  Yadda aka yi wa wasu 'yan mata tsirara a hotunan da AI ya kirkira

Sannan a halin da muke ciki a Nigeria ya dace ace rundinar tsaron Nigeria tana da security emergency control center, ta yanda idan anyi garkuwa da mutane ko anyi ambush kafin a samu wasu awanni an dauki matakin gaggawa a kuma samu sharing of ideas daga experts, idan na samu lokaci zanyi cikakken bayani akan yadda ake gudanar da security emergency control center Insha Allah

 

Bayan haka, a baya na taba yin bayani akan e-security ta yanda za’a kirkiri wata software application domin jami’an tsaron Nigeria suyi amfani dashi wajen samun kariya daga fadawa tarkon ambush

 

Idan an kirkiri manhajar za’a hadata da Google Earth ne, sannan a saka sensor detective na siffar mutane da kowani irin lethal barrel wato makami da zai iya yin kisa, da sensor na kayan explosive

 

Wato misali za’a sauke application din akan waya ko computer, da zaran an budeshi, zai nuna maka duk abinda ke gabanka wanda ya hada da mutum, makami da kayan fashewa, to kunga wannan an samu kariya mai karfi daga fadawa tarkon ambush

APPLY NOW!  Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Wa Dakarun Ta Kashedi

 

Kamar shekaru 3 da suka wuce na taba rubuta takarda na kaiwa masu iko da tsaro a Abuja, na nemi a bamu dama mu kirkiri wannan manhaja na electronic security, idan zaku tuna har anan dandalin Facebook nayi rubutu akan muhimmancinsa, kuma ba wani kudi mai yawa za’a kashe ba, amma basu kula ba

 

Wato abinda yake faruwa a Kasarnan game da sha’anin tsaro, idan ka tsaya ka dubeshi da kyau zaka fahimci akwai cin amana ne sai kuma ya zama harka na kasuwanci, domin a lokacin da akace ga matakin da ya kamata a dauka sai akaki a dauka to ya zama cin amana, ana so ta’addancin ya cigaba da wanzuwa ne saboda akwai manyan jami’ai da suke samun kudi da haka

 

Don haka mu cigaba da addu’ah, Allah Ya kawo mana ranar da zamu samu Shugabanni masu imani da tausayi wanda zamu basu shawara akan tsaro su karba kuma su aiwatar

 

APPLY NOW!  Su wane ne kusoshin gwamnatin Tinubu?

Muna rokon Allah Ya kare mana dukkan jami’an tsaron Nigeria, Ya tabbatar musu da nasara akan ‘yan ta’adda Ya tona asirin wadanda suke cin amana

 

Datti Assalafy