Labarai

Girgizar Kasa Ya Hallaka Dalibai A Morocco

Girgizar Kasa Ya Hallaka Dalibai A Morocco Cewar malamar makaranta

“Na shiga tunanin ina riƙe da rajistar ɗalibai ina jan layi kan sunan ɗalibai ɗaya bayan ɗaya, har sai da na goge sunaye 32; waɗanda duk sun mutu.”

 

Nesreen Abu ElFadel, malamar da ke koyar da darasin Arabiya da Faransanci a Marrakesh, tana tuna yadda ta ruga zuwa ƙauyen Adaseel da ke kan tsauni a Morocco, tana ƙoƙarin tono ɗalibanta daga ɓaraguzai bayan girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6.8 da ta afka wa ƙasar.

APPLY NOW!  Dalibi ya ratsa ƙasashe shida a kan keke don shiga Jami'ar Al-Azhar

 

Nesreen da mahaifiyarta a kan titi suke barci bayan girgizar ƙasar ta ranar Juma’a.

 

Bayan ta ji labarin girman ɓarnar da girgizar ƙasar ta yi wa ƙauyen, nan take ta fara tunanin makarantar da take koyarwa – makarantar Adaseel da kuma ɗalibanta waɗanda take kira ‘ya’yanta.

 

“Na tafi ƙauyen kuma na fara tambayar yaran: ina Somaya? Ina Youssef? Ina waccan yarinyar? Ina wannan yaron? Daga baya ta ji labarin cewa dukkaninsu sun mutu.

APPLY NOW!  A karon farkon tawagar ECOWAS ta gana da Bazoum

 

A ranar 8 ga watan Satumba, aka samu mummunar girgizar ƙasa da ba a taɓa samu ba a Morocco, kuma mafi muni a shekaru 60 inda mutum kusan 3,000 suka mutu.

 

Mummunar girgizar kasar ta fi yin illa a kudancin Marrakesh, inda ta lalata ƙauyukan da ke kan tsaunuka.

 

An samu gawar ɗaya daga cikin ɗaliban da suka mutu – masu aikin ceto sun samu gawar Khadija kwance kusa da ɗan uwanta Mohamed da ƴan uwanta mata Mena da Hanan, dukkansu a kwance saman gado, watakila suna barci lokacin girgizar ƙasar, kuma dukkaninsu dalibai ne a makarantar Nesreen.

APPLY NOW!  Gwamnan ya ba da umarnin raba shinkafa buhu 40,000 don rage radadi

 

“Khadija ce ɗalibar da na fi ƙauna, tana da ƙoƙari da basira kuma tana son rera waƙa. Tana zuwa gidana kuma ina son koyar da ita da kuma magana da ita.

 

Nesreen ta tuna ɗalibanta da ta kira masu biyayya da ke son karatu.

 

Duk da talauci da tsadar rayuwa amma hakan bai hana yaran zuwa makaranta ba “wani muhimmin abu a duniya.”

APPLY NOW!  AN FASA RUMBU A ADAMAWA

 

“Ranar Juma’a da dare ne darasinmu na ƙarshe, sa’a biyar kafin girgizar ƙasar, a cewar Nesreen.

 

“Muna karanta taken Morocco, wanda muke son rerawa a gaban dukkanin ƴan makaranta a ranar Litinin.

 

Duk da nuna juriya, amma Nesreen na fama da matsalar tunani. Har yanzu ba ta iya manta abin da ya faru da ɗalibanta da makarantarta.

APPLY NOW!  Manyan Jahohi 19 da ke Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa

 

“Ba na iya barci, ina cikin kaɗuwa,” in ji ta.

 

“Mutane na cewa na tsallake rijiya da baya, amma ban san yadda zan iya ci gaba da rayuwa ba.”

 

Nesreen na matuƙar son koyar da yara Larabci da Faransanci a Adaseel, ƙauyen da ke da yawan ƴan ƙabilar Amazigh masu rinjaye a arewacin Afirka waɗanda ke magana da harshensu na asali Tamazight.

APPLY NOW!  Anfani da fetur a Najeriya ya ragu kashi 35 cikin 100

 

“Larabci da Faransanci na da wahalar koyo, amma yaran suna da basira, kusan ma sun laƙanci harsunan,” a cewarta.

 

Nesreen na son ci gaba da aikinta na koyarwa – tana fatan za a sake gina makarantar Adaseel, da ta girgizar ƙasa ta ɗaiɗaita.

 

Cibiyoyin ilimi 530 girgizar ƙasar ta lalata, wasunsu sun yi muni, kamar yadda alƙalumman hukuma suka nuna.

APPLY NOW!  Denmark zata haramta ƙona Alkur'ani Mai Girma

 

Gwamnatin Morocco ta rufe makarantu a yankunan Al-Houz, Chichaoua da Taroudant girgizar ƙasar ta fi muni.

 

“Ƙila wata rana idan sun gina makarantar an dawo karatu, za mu yi bikin karrama ɗaliban 32 tare da bayar da labarinsu,” in ji Nesreen.