Labarai
A karon farkon tawagar ECOWAS ta gana da Bazoum
Tawagar ECOWAS kungiyar kasashen yammacin Afrika, ta samu nasarar ganawa da hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum.
Ziyarar na zuwa ne kwana guda bayan kammala taron hafsoshin sojojin kasashen da ke karkashin kungiyar ECOWAS ta gudana a Ghana, inda suka bayyana aniyarsu ta yin amfani da karfin soji wajen maida gwamnatin farar hula, muddin sojojin Nijar din suka ci gaba da yin turjiya gameda matakan diflomasiya da ECOWAS ke dauka don warware rikicin.