Shugaban Wagner Prigozhin ya mutu a hatsarin jirgi
Shugaban Wagner sojojin hayar nan ta Wagner, Yevgeny Prigozhin ya mutu a wani hatsarin jirgin sama, tare da ƙarin mutum tara a cikin jiragen sama a Rasha.
An yi imani yana cikin jirgin saman da ya faɗi.
Tun da farko, wani zauren Telegram mai suna Grey Zone ya ba da rahoton cewa an harbo jirgin ne da wasu makaman kakkaɓo jiragen sama a yankin Tver, na arewacin birnin Moscow.
Jirgin saman, wanda ya tashi daga Moscow zuwa birnin St Petersburgh, ɗauke da fasinjoji guda bakwai Masu karan kwana da ma’aikatan jirgi uku.
Prigozhin ya jagoranci wani boren sojoji da bai yi nasara a kan rundunar sojin Rasha a cikin watan Yuni.
Shafin Telegram na Grey Zone ya ruwaito mazauna yankin na cewa sun ji ƙarar fashewar wani abu har guda biyu kafin ma faɗuwar jirgin, kuma sun ga tururi guda biyu a lokacin wanda Ake zargin makamin da aka harba ne.
Kamfanin dillancin labarai na Tass ya ce jirgin saman ya kama da wuta a lokacin da ya faɗi a ƙasa, inda ya ƙara da cewa tuni aka gano gawawwakin mutum huɗu cikin Jirgin.
Ya ce jirgin ya yi tafiyar da batakai rabin sa’a bayan tashinsa sannan aka buge Jirgin.
Kamfanin dillancin labarai na Rasha Interfax ya ruwaito ma’aikatar ba da agajin gaggawa na cewa ana kyautata tsammanin dukkan mutanen da ke cikin jirgin saman sun mutu, lokacin da ya faɗo ƙasa bisa hujjojin yadda Jirgin ya Zama.
Ma’aikatar ta ƙara da cewa jirgin ya rikito ƙasa ne a kusa da unguwar Kuzhenkino a lardin dake Tver.
Rahotanni sun ce an gano gawawwakin mutum takwas a wurin da jirgin ya faɗo, haka zalika, anma babu tabbaci a kan cewar Yevgeny Prigozhin yana cikin jirgin saman a Hukumance.
Yevgeny Prigozhin shi ne shugaban kamfanin sojojin hayar Wagner, wanda ya kafata a shekara ta 2014.
Hamshaƙin ɗan kasuwa ne da ke da tarihin aikata laifuka, ana yi masa inkiya da “Mai dafa wa Putin abinci” saboda yana samar da abinci ga fadar Kremlin.
A watan Yuni ne, ya jagoranci dakarunsa wajen gudanar da wani boren sojoji na taƙaitaccen lokaci, bayan ya ƙwace iko da birnin Rostov-on-Don na kudancin Rasha kuma ya tunkari birnin Moscow, da niyyar hamɓaras da shugabannin sojojin ƙasar.
Tun lokacin da ya jagoranci boren sojoji zuwa Moscow a ƙarshen watan Yuni, masu lura da al’amura da yawa a Rasha suka yi wa shugaban kamfanin Wagner nan, Yevgeny Prigozhin laƙabi da “Gawa tana tafiya”.
Martanin Shugaba Putin na farko ga ƙalubalantar shugabannin tsaron Rasha, cike yake da ɓacin rai, inda ya bayyana lamarin da cin amana da kuma yankan baya a cikin wani saƙon bidiyo da ya fitar ranar 24 ga watan Yuni.
Kuma duk da yake, cikin sauri an cimma yarjejeniyar da ta bai wa Prigozhin ci gaba da watayawarsa kuma daga bisani ya tafi Belarus, kafin ya koma birnin St Petersburg da kuma wannan mako, inda aka gan shi a wani wuri a Afirka, hakan ba ya nufin cewa yaba cikin aminci.