Labarai

Masu Tonon Ma’adanai 30 sun Mutu Bayan Ruftawar Kasa

Masu Tonon Ma'adanai 30 sun Mutu Bayan Ruftawar Kasa

Masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba 30 ne suka mutu bayan ƙasa ta rufta kansu a ƙaramar hukumar Kuje da ke Abuja babban birnin Najeriya.

Shugaban ƙaramar hukumar ne ya bayyana haka ranar Alhamis a lokacin da shugabannin ƙananan hukumomin birnin suka gana da ministan Abuja, Nyesom Wike.

Haka kuma masu garkuwa da mutane sun sace mutum 19 ranar Alhamis a yankin ƙaramar hukumar Bwari da ke Abuja babban birnin Najeriya.

Ministan – wanda ya nuna damuwarsa game da waɗannan batutuwa – ya ce zai gayyaci daraktan hukumar tsaron farin kaya da kwamishinan ‘yan sanda birnin domin ɗaukar matakan da suka dace don kuɓutar da mutanen.

Mista Wike ya kuma yi kira ga shugabannin ƙananan hukumomin da su kafa kwamitocin sa ido a ƙananan hukumominsu domin lura da ayyukan masu haƙar ma’adinai.

Ya kuma ce a nasa ɓangare zai gana da ministan ma’adinai Dele Alake domin kawo ƙarshen ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a Abuja.

APPLY NOW!  Gwamnatin Najeriya Za Ta Sake Gurfanar Da Emefiele Kan Wasu Sabbin Tuhume-tuhume