Mansura Isah ta fashe da kuka lokacin da ta ziyarci gidan yaron da wata mata taiwa Video tana zagin halittar sa.
ALLAHU AKBAR: Tsohuwar Jarumar Kannywood Mansura Isah ta fashe da kuka lokacin da ta ziyarci gidan yaron da wata mata taiwa Video tana zagin halittar sa.
A kwanakin baya ne wata mata ta ɗora hoton wani yaro mai suna Halifa dake fama da cuta inda ta rinƙa zagin halittar sa tana tambayar da shi mutum ne ko ba mutum ba.
A Videon anji yadda yaron ke ce mata shi mutum ne, amma ta daga saiya bar mata gida a dole dan ta gaji da ciyar dashi amma koda yaushe a bushe.
Videon ya dauki hankali a kafar sada zumunta na TikTok inda jama’a da dama suka tausaya wa yaron, tare da neman inda yake.
Jaridar AMINTACCIYA ta ci karo da yadda tsohuwar Jarumar Kannywood Mansura Isah ta bayyana takaicin ta a shafin ta na TikTok.
Mansura isa ta nemi duk wanda yasan inda matar take ya faɗa za’a bashi dubu hamsin 50k idan ya bayar har Number ta za’a bashi dubu saba’in 70k.
A binciken da wani mai rajin taimakon marasa karfi a TikTok Aminu J. Town ya gudanar ya bayyana cewa sun gano matar kuma an damaƙa ta a hannun hukuma.
A cewar sa tuni yaron ya fara karbar magani, a lokacin da Mansura Isah ta je gidan su yaron don tallafa masa tare da cigaba da kula da lafiyar sa ta fashe da kuka duba da irin halin da ta sami yaron.
Mansurah Isa taci alwashin tallafawa yaron don ganin rayuwar sa ta inganta bayan nema masa lafiya.