Labarai
A karon farkon tawagar ECOWAS ta gana da Bazoum
Tawagar kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS, ta samu nasarar ganawa da hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum.
Janar Abdulsami Abubakar Mai Ritaya, da mai alfarma Sarkin Musulmi na kasar Muhammad Sa’ad Abubakar, suka sake komawa kasar don gudanar da tattaunawa gameda juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar saboda gudun afkuwar Yaki.
Ziyarar na zuwa ne kwana guda bayan kammala taron hafsoshin sojojin kasashen da ke karkashin kungiyar ECOWAS da ya gudana a Ghana, inda suka bayyana aniyarsu ta yin amfani da karfin soji koda yaushe domin maida gwamnatin farar hula, muddin sojojin Nijar din suka ci gaba da yin turjiya gameda matakan diflomasiya da ECOWAS ke dauka don warware rikicin.
Muna fatan Allah yasa a samu Maslaha.
Kuyi sharing domin Yan uwa su anfana