Labarai

An rataye mutum uku da suka kai harin bam da ya kashe sama da mutum 300

An rataye mutum uku da suka kai harin bam da ya kashe sama da mutum 300

Kasar Iraqi ta rataye wasu mutum uku da aka samu da hannu a harin bam da aka kai a birnin Bagadaza.

 

Kasar Iraƙi ta rataye wasu mutum uku da aka samu da hannu a harin bam da aka kai a birnin Bagadaza.

 

Wannan harin bam ya faru ne a cikin shakarar 2016 a cikin watan azumi kuma ya kashe mutane sama da 300 tare da jikkata wasu da dama.

 

Wannan dai shi ne harin bam mafi muni da aka kai a Iraki tun bayan mamayar da Amurka ta yi a shekara ta 2003.

 

An aiwatar da hukuncin kisan ne a ranar Lahadi ko Litinin, in ji ofishin Firayim Minista Mohammed Shia al-Sudani.

 

Amma dai ba a bayyana sunayen wadanda aka kashe ba.

 

Firaministan ƙasar ya shaida wa iyalan wadanda abin ya shafa cewa an zartar da hukuncin kisa kan mutanen da ke da hannu a tashin bam din.

See Also  Yan Boko haram kusan 100 sun mutu a fadan Suyasu