Labarai

Me ‘yan Najeriya ke cewa kan ma’aikatun ministocin Tinubu?

Me 'yan Najeriya ke cewa kan ma'aikatun ministocin Tinubu?

Bayan shafe kimanin kwana tamanin a kan mulki, a ranar Litinin mai zuwa Shugaba Bola Tinubu zai rantsar da ministocinsa 45 da majalisar dattijan Najeriya ta tabbatar.

 

Wannan wata manuniya ce cewa, gwamnatin Tinubu ta gama tsayuwa, inda za ta kama aiki gadan-gadan.

 

Ma’aikatun da aka bai wa ministocin mafi ba-zata, akwai ta kula da babban birnin tarayya Abuja, wadda aka tura Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ɗan jam’iyyar adawa ta PDP. Karon farko kenan da wani mutumin kudancin Najeriya zai jagoranci ma’aikatar, aƙalla tun bayan komawar ƙasar mulkin dimokraɗiyya a 1999.

APPLY NOW!  An Sace Kwamishinan 'yan sanda a Jihar Benue

 

Tuni dai masharhanta da waɗanda ake mulka ke ci gaba da tsokaci a kan adadi da girman ma’aikatun da aka bai wa yankunansu a ƙasar.

 

Wasu masana a Najeriya dai, na ganin bisa dukkan alamu, yankin kudu maso yammacin Najeriya ne ya fi yin kane-kane da caɓawa a rabon ma’aikatun.

Suna ganin da wannan dama, sashen zai iya kankane harkokin tattalin arziki da na siyasar Najeriya.

APPLY NOW!  Faɗa Ko Gasar Technology Tsakanin China Da America

Wani masanin kimiyyar siyasa ya shaida wa BBC cewa, wani abu da za a iya fahimta game da rabon ma’aikatun shi ne shugaban ƙasar ya fifita ɓangaren da ya fito na Kudu maso Yamma.

Skip podcast promotion and continue reading

Korona: Ina Mafita?
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

APPLY NOW!  Abubuwan da za su sa auren ku ya yi karko

Kashi-kashi
End of podcast promotion
Sai dai, gwamnati ta musanta zargin, tana cewa bisa al’ada mataimakin shugaban ƙasa ne yake tafiyar da harkokin tattalin arziƙi a Najeriya. Kuma Shugaba Tinubu bai canza wannan al’amari ba.

Farfesa Abubakar Kari na jami’ar Abuja, ya ce muƙaman ministocin ta wani bangaren bai zo da mamaki ba, yayin da ta wani fanni yake da ban mamaki.

APPLY NOW!  Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Wa Dakarun Ta Kashedi

Ya ce, ko fizge idan aka duba, za a ga manyan ma’aikatu masu tasiri a ɓangaren tattalin arziƙi kimanin shida duk sun tafi hannun ministocin da suka fito daga yankin na Shugaba Tinubu. Ma’aikatun sun haɗar da;

 

A cewar Farfesa Kari, waɗannan, ma’aikatu ne masu manyan hukumomi da ke da tasiri a fannin tattalin arziƙi a ƙarƙashinsu.

APPLY NOW!  Denmark zata haramta ƙona Alkur'ani Mai Girma

Ya ce dukkan ma’aikatun, ba ma a ƙasashe masu tasowa ba, hatta ƙasashe masu ci gaban arziƙi kusan su ne manyan masu tafiyar da harkokin tattalin arziƙin ƙasa.

Duk ɓangaren da ke da waɗannan ma’aikatu a ƙarƙashin ikonsa, in ji Farfesa Kari, to shi ke riƙe da ragamar tattalin arziƙin ƙasa, wanda kuma yake riƙe da akalar tattalin arziƙi, to shi ne zai iya sarrafa akalar siyasa.

APPLY NOW!  Majalisar Dattawan Najeriya ta tantance ministoci 14 cikin 28

Martanin Gwamnatin Tarayya
Sai dai, babban mataimaki na musamman ga shugaban Najeriya kan yaɗa labarai, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce zargin ba gaskiya ba ne.

A cewar, ga duk wanda ya san yadda harkar mulki take tafiya a Najeriya, ya san cewa mataimakin shugaban ƙasa ne yake gudanar da harkokin tattalin arziƙin ƙasa.

APPLY NOW!  Hon, Mannir Babba Ɗan Agundi Yayi Nasara A Kotu Inda Ta Tabbatar Masa Da Kujeran Sa.

Kuma ga majalisar kula da tattalin arziƙi ta ƙasa wadda duk gwamnonin arewa 19 ke ciki, “to da wannan ta yaya za a danne arewa?” Abdul’aziz ya tambaya.

Ya ce akwai hukumomi da yawa masu tasiri a fannin tattalin arziƙin Najeriya da ke ƙarƙashin ‘yan arewa, inda ya bayar da misali da hukumar hana fasa-ƙwauri (kwastam).

APPLY NOW!  Manyan Jahohi 19 da ke Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa

Jami’in ya ce, “a halin yanzu yankin arewa yana fama da muhimman matsaloli guda biyu ne, tsaro da ilimi, to idan ka duba za ka ga duk ma’aikatun waɗannan fannoni, an damƙa su ne ga ‘yan arewa.”

Bayan rabon ma’aikatu ga ministocin, ya ce akwai kuma hukumomin tsaro na ‘yan sandan ciki wato DSS da hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasa NIA dukkansu suna ƙarƙashin jagorancin ‘yan arewa.

APPLY NOW!  Najeriya da Kanada za su hada kai don

Ya ce akwai kuma buƙatar bunƙasa ayyukan gona wanda arewa ta dogara da shi, ‘’to wannan ma an bai wa mutumin arewa ne.”

Hadimin na shugaban Najeriyar ya ce, a tsarin mulki, ba ɓangaren zartarwa ba ne kaɗai yake da iko, akwai majalisar dokoki, wadda ke tabbatar da cewa ɓangaren zartarwa, bai yi wani abu da zai tauye wani ɓangare da ma ɗaukacin ƙasar ba, inda kowa yake da wakilci.

APPLY NOW!  Laifin Me Maryam Shatty Tayi Aka Cire ta a minista??

Sannan ya ce hatta ita kanta majalisar zartarwa ta ƙasa idan aka duba yawan mambobinta za a ga cewa ‘yan arewa sun fi yawa a cikin wannan majalisa wadda ta ƙunshi ministoci, kuma sai abin da majalisar ta amince da shi ne ɓangaren zartarwa zai aiwatar.

 

Sauran Ministoci
Wasu daga cikin ministocin da Shugaba Tinubu ya bai wa ma’aikatu sun haɗar da, tsohon gwamnan jihar Jigawa na baya-bayan nan Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar.

APPLY NOW!  Ƴan sanda sun kama mutum 20 bisa zargin garkuwa da mutane

Wasu masu sharhi na ganin naɗin tsohon gwamnan a matsayin ministan tsaro ya zo da mamaki, kasancewarsa ɗan siyasa kuma fitaccen ɗan kasuwa.

Ba a san shi da wata ƙwaƙƙwarar alaƙa ko aiki na tsaro ba.

Sai dai, ba shi ne mutum na farko ba, wanda ba shi da tarihin aikin tsaro a baya, da aka taɓa bai wa muƙamin ministan tsaron Najeriya.

APPLY NOW!  Gwamnatin Najeriya tayi bayani akan shiri na sake dawo da tallafin mai

Shi da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ne, wanda aka bai wa ƙaramin minista, za su jagoranci ma’aikatar tsaron Najeriya.

A karon farko kuma, tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ɗan jam’iyyar PDP daga kudancin Najeriya zai jagoranci babban birnin tarayyar ƙasar, Abuja.

Ma’aikatar albarkarun man fetur ta samu Heineken Lokpobiri a matsayin ƙaramin minista, sanarwar rabon ma’aikatun dai ba ta ambaci wanda zai riƙe mukamin babban ministan man fetur ba.

APPLY NOW!  Su wane ne kusoshin gwamnatin Tinubu?

Hakan dai ya sa, wasu sun shiga raɗe-raɗin cewa tamkar magabacinsa, shi ma Tinubu mai yiwuwa shi ne zai kasance babban ministan man fetur.

Ita kuwa ma’aikatar shari’a ta fada hannun Lateef Fagbemi.

Wasu daga cikin sauran ministocin sun hada da:

Ma’aiktar yada labarai da wayar da kan jama’a – Muhammad Idris

APPLY NOW!  NDLEA ta kama dala miliyan 20 da take zargin na boge ne

Ministan Ilimi -Yusuf T. Sununu

Karamin ministan gidaje da raya birane -Abdullahi T Gwarzo

Ministan ayyukan gona da samar da abinci -Abubakar Kyari

Ministan Ilimi – Tahir Mamman

Ministan harkokin cikin gida -Sa’idu Alkali

Ministan harkokin waje – Yusuf Tuggar

Ministan lafiya – Farfesa Ali Pate

Ministar al’adu – Barista Hannatu Musawa

APPLY NOW!  Dalibi ya ratsa ƙasashe shida a kan keke don shiga Jami'ar Al-Azhar

Ministan wasanni – John Enoh

Ministan sufurin jirgin sama – Festus Keyamo

Karamar ministar Abuja – Mairiga Mahmud

Ministan Ilimi da fasaha – Uche Nnaji

Ministar harkokin mata – Uju Kennedy

Ministan ayyuka – David Umahi