
Baya ga mutuwa da yunwa, waɗanda ɗan Adam ya kasa yi wa kansa maganinsu, akwai kuma mace-macen aure duk da ɗumbin litattafai da maƙaloli da wa’azuzzuka da ake yi da zimmar magance ta.
A kowace rana akan ɗaura dubban aure ko fiye da haka a cikin kusan kowace al’umma a duniya. Sai dai yayin da ake ɗaura dubbai kullum, haka ma dubbai ke mutuwa a kowace rana.
A jihar Kano kaɗai, aure 999 ne suka mutu cikin wata tara na farkon 2023, a cewar wani rahoto da reshen ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta duniya na Kano ya fitar a wannan makon.
Ta samu waɗannan alƙaluma ne bayan ta karɓi ƙorafi 1,080 daga ma’aurata, wanda ya ninninka na 2022 da ta karɓa (288).
A 2020, hukumar Hisbah ta Kanon ta ce aure 631 ne suka mutu, yayin da wani bincike na Mujallar International Journal of Social Science and Humanity da aka yi a 2009 ya ce akwai sama da zawarawa miliyan daya da aurensu ya mutu a jihar.
Idan muka duba matsalar a Najeriya, abu ne mawuyaci a iya samun alƙaluman da ke nuna yawan rabuwa ko kuma sakin aure, ko kuma yawan zawarawa maza da mata.
Amma dai a alƙaluman hukuma, wani rahoto na hukumar ƙididdiga ta ƙasa wato National Bureau of Statistics (NBS) ta wallafa a 2016 ya ce kashi 0.2 cikin 100 na maza da kuma 0.3 na matan Najeriya ne suka raba aurensu a kotu.
Sai dai kuma, bayan kasancewar rahoton tsoho, shakka babu adadin auren da ke mutuwa sun ninninka haka kasancewar har yanzu aure-auren da ake ɗaurawa a wajen kotu sun ninninka na kotun, haka ma waɗanda ke mutuwa.
Ganin cewa matsalar na neman ta gagari Kundila, ko me ya kamata ma’auratan su din ga yi don yauƙaƙawa da kuma guje wa lalacewar auren nasu?
Mun tuntuɓi Sheikh Ibrahim Khalil, malamin addini a Kano, da kuma Maijidda Labo Mahuta, wata mai koyarwa da bayar da shawarwari kan zaman aure da soyayya a Abuja, don jin amsar wannan tambaya.
Abubuwa biyar daga Sheikh Ibrahim Khalil
Shahararren malamin addini a Kano – wanda kuma yake gabatar da shirye-shirye da dama a gidajen rediyo game da zamantakewa -ya zayyana abubuwa biyar da yake ganin su ne kan gaba wajen magance matsalar rabuwar aure.
Haƙuri: “Haƙuri ne ke riƙe aure. Miji da mata su zama masu haƙuri. Miji ya daina garaje wajen yin saki, ita kuma mace ta daina hasala.”
Kalmomi masu kyau: “Lallai ne miji ya sani cewa kalmomi masu daɗi ne ke zaunar da aure lafiya. Ya dinga yabonta, yana ziga ta, yana koɗa ta, yana tausasa mata.
“Musamman a yanzu da ake cikin wani hali, ya dinga ba ta haƙuri, yana kwantar mata da hankali.”
Daina kai wa iyaye ƙara: “Lallai ne su daina kai wa magabatansu ƙara, su daina saka wani mutum na uku a tsakaninsu a harkar aure.”
Fahimtar juna: “Abin da ke zaunar da aure lafiya shi ne fahimtar juna. Mace ta gane abin da mijinta ba ya so ta bari, shi kuma ya yi ƙoƙarin yaba mata a kan kowane abu.”
Kar a yi hukunci lokacin fushi: “Idan suna cikin fushi kar wani daga cikinsu ya yi wani hukunci. Idan namijin ne ya yi fushi ta ƙyale shi ya huce sannan su yi magana.
“Idan ita ce ta yi fushin ya bari ta huce sannan su yi magana. Amma a daina garajen saki, ko garajen kai ƙara wajen iyaye, ko kai ƙara kotu, ko wani wuri.”