Nishadi

Matar da Take Cinye Buhun Masara a kwana kadan Auren ta ya Mutu

Matar Da Take Cinye Rabin Buhun Masara Ita Kaɗai A Mako Ɗaya Auran Ta Ya Mutu.

Daga Fatima Nuraddeen Dutsin-ma.

A wani rahoto da muke samu na wata mata mai suna Angela cewa mijin ta ya dirƙa mata saki biyo bayan yadda ciyar da ita ya gagaresa.

Mijin nata mai suna Daniel ɗan asalin Jihar Imo ya shaida wa Manema Labarai a ranar laraban da ta gabata cewa shi yayi iya ƙoƙarinsa na wurin ɗaukan nauyin matarsa kuma yayi kira ga iyayen ta da suma su zo domin haɗa kai dan ciyar da ɗiyar su amma suka yi kunnen Uwar Shegu da shi.

APPLY NOW!  Best Photo: Hoto mafi kyau a Juma'a 29-Sep-2023

Matar da take Cinye Buhun Masara a kwana kadan Matar da take Cinye Buhun Masara a kwana kadan

Daniel dai ya auri Angela ce a matsayin bazawara bayan rabuwar ta da ainihin mijinta wanda bai bayyana mana dalilin rabuwan nasu ba.

Bugu da kari ya ƙara Bayyana wa manema labarai cewa a mako ɗaya kawai matar tana cinye rabin buhun Masara ita kaɗai, idan kuma shinkafa za’a girka ita kaɗai kawai take tada tiya ɗaya da rabi daga safe zuwa dare, ɓangaren ruwa kuma tana iya shanye ruwa leda biyar na fiyo wata Cikin kwana Uku rigis, kifi ko Nana kuma ba’a maganarsu, a bisa waɗannan dalilan yasa mijin nata ya haƙura da ci gaba da zama da ita.”

APPLY NOW!  Cristiano Ronaldo Yana Burin Zuwa Dakin Ka'aba