Abun da ke haddasa tsananin mutuwar aure a Kano?
Abun da ke haddasa tsananin mutuwar aure a Kano?
Ana ci gaba da bayyana damuwa bayan wani rahoto da kwamitin kare haƙƙin ɗan’Adam ya fitar da ke cewa a bana kawai, aure kusan dubu ɗaya ne ya mutu a Kano.
Adadin mace-macen auren da kwamitin ke tattarawa, ya ninka, wanda aka samu bara.
“Galibin waɗanda auren nasu ya mutu matasa ne, yawanci kuma ƴaƴansu ba su wuce biyu ko uku ko huɗu ba.”, in ji wani jami’in kwamitin.
Mai yiwuwa ne kuma akwai ƙarin aurace-auracen da suka mutu a Kano, amma batun bai zo hannun wannan kwamiti, mai bibiya da kare haƙƙoƙin mutane, musamman ma dai mata a tsakanin al’umma ba.
Lamarin dai na ƙara fito da buƙatar wayar da kai da ɓullo da tsare-tsaren da za su taimaka wajen rage mace-macen aure.
Kwamitin ya ce ya kai ga wannan ƙididdiga ce daga ƙorafe-ƙorafen da ya samu kai tsaye daga ma’aurata a matakan ƙananan hukumomin jihar, da kuma shari’o’in saki da suke bibiya a kotuna.
Rahoton ya ce bayanan da ya tattara da kuma ƙorafe-ƙorafen da ya samu daga ma’aurata a sassan jihar ta Kano daga farkon shekarar nan zuwa yanzu, ya kai 1,080, abin da ya rubanya wanda aka samu a bara.
Jami’in kwamitin, kwamared Hafiz Sunusi Sanka ya shaida wa BBC cewar al’amarin sakin aure ya tsananta fiye da tunani.
Ya kuma ce yanzu haka akwai wasu shari’o’i na sakin aure da ake tafkawa a kotuna daban-daban da ke faɗin jihar.
Aure nawa ya mutu a 2022 da 2023
Sanarwar da ƙungiyar ta fitar ta ce “Korafe-korafen da suka shafi auratayya da ma’aurata da suka samu, kuma ta yi aiki a kai, sun kai 288 a shekarar 2022, amma a 2023 da muke ciki matsalar ta yi tashin gwauron zabi.
Kawo yanzu, ƙungiyar ta ce ta karɓi ƙorafe-ƙorafe daga ma’aurata da suka kai 1,080, kusan ninki huɗu ke nan na abin da suka samu a 2022.”
“Cikin wannan adadi na 1,080, aure 999 ne ya mutu, wato sama da kashi 90 cikin ɗari na adadin ƙorafin da kwamitin ya samu.
Yayin da rigimar aure 50 (da ta zo hannunsu) ke gaban kotuna daban-daban.” A cewar bayanin ƙungiyar.
Dalilan mutuwar aure a Kano’
Ƙungiyar ta bayyana cewa ta gano wasu abubuwa da suka zama sanadin yawan mace-macen aure a jihar.
Wasu daga cikin dalilan da ta zayyana a bayanin nata su ne:
Me al’ummar Kano ke cewa kan yawan mutuwar aure?
Wasu daga cikin waɗanda BBC ta tattauna da su sun bayyana gajen haƙuri a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da ke iza wutar mace-macen aure.
Wani mazaunin Kano ya ce “Haƙuri ya yi ƙaranci, shekara 15 a baya, abin bai yi munin haka ba, idan ba a kai zuciya nesa ba, za ka ga irin waɗannan matsaloli(n zamantakewa) suna ta faruwa”.
Wata kuma ta alaƙanta mace-macen auren a kan ƙarancin ilimin zamantakewa da kuma haɗama.
“Wasu matan ba su da tsafta, kuma ba biyayya, su kuma maza, wani bai gama wadatar da gidansa da abubuwan buƙatu ba, amma sai ya ƙaro aure,” in ji ta.
Haka zalika, sun bayyana taɓarɓarewar tarbiyyar al’umma, a matsayin ɗaya daga cikin matsalolin da ke haddasa rabuwar aure.
Yawaitar mutuwar aure babbar matsala ce da ta daɗe tana addabar jihar ta Kano da ma wasu jihohi a arewacin Najeriya.
Yanzu haka ɗaya daga cikin manyan ayyukan da gwamnatin jihar Kano ta sanya a gaba shi ne auren zawarawa.
A shekarar 2012 ne, gwamnatin Rabi’u Musa Kwankwaso ta ɓullo da shirin aurar da zawarawa, a wani ɓangare na tallafa wa matan da aurensu ya mutu.