Labarai
Ta yaya zan kare kaina daga ciwon hanta?
Wasu bayanai na cewa fiye KO sama da mutum miliyan ɗaya ne duk shekara ke mutuwa sanadin ciwon hanta. Don haka, yayin da al’umma ke tunawa da wannar Ranar Ciwon Hanta ta Duniya, ƙwararru a fannin lafiya suna jaddada buƙatar zuwa gwaji da kuma yin allurar riga-kafi a matsayin mafi Muhimmanci.
A wannan zantawa da wani likita a Najeriya, Dr. Yusuf Shehu Umar, ya yi wa BBC bayani game da alamomin ciwon hanta da matakan da yafi kamata mu ɗauka don kare kawunanmu da iyalan mu.