Yadda zai faru idan aka kwace kujeran Gwamna a Kotun Gaba
Yadda zai faru idan aka kwace kujeran Gwamna a Kotun Gaba
Idan Shari’ar zabe ba tayi mun dadi ba a matsayina na ‘dan takara me ya kamata nayi bayan Tribunal (Kotun sauraren kararrakin zabe) bata bani gaskiya ba?
_________________________
A tsarin dokokin Nigeria idan Kotu tace baka ci zabe ba kana da damar daukaka ‘kara. Amma ina so mu sani, Appeals wato daukaka ‘kara da suke alaka da zabe a Nigeria sun kasu kashi biyu, idan akan Kujerar shugaban kasa ko Kujerar Gwamna ake takaddama akai toh zaka iya daukaka ‘kara ne zuwa Court of Appeals da kuma Supreme court kadai.
~ Idan kuma Kujerar Sanata ne, Reps ko Kujerar Member State House of Assembly toh zaka iya daukaka ‘kara ne zuwa Court of Appeal kadai. Wannan ne yasa baka jin ‘kararrakin dake alaka da zaben Sanata, House of Reps da state House of Assembly basa zuwa Supreme Court (Kotun ‘Koli).
Section 285 subsection 7 na 1999 Constitution yace “Idan aka daukaka ‘kara akan zabe toh dole Kotun da aka shigar mata da karar ta yanke hukunci a cikin kwanaki 60, daga ranar da aka daukaka ‘karar zuwa gare ta”.
~ Wannan section din yana bayyana maka cewa idan kayi Appeals har kwanaki 60 suka wuce Kotun bata ce komai akai ba toh Kotun bata da ikon dawowa ta yanke hukunci akai.
Yaushe ake shigar da Appeal? wato yaushe ake daukaka ‘kara?
Section 2 of the Supreme Court and Court of Appeals Election Appeal Proceedings Practice Direction 2023 yana cewa:
“Wanda zai ‘daukaka ‘kara toh yayi a cikin kwanaki 14 daga ranar da Trial Court wato Kotun farko (Tribunal) ta yanke hukuncin akan wannan ‘karar”.
(Wannan fassara na ne, ba haka yazo kai tsaye a cikin Section din ba, na saka shi haka ne don a fahimci abun).
Abinda wannan gabar take nufi shine, idan kwanaki 14 suka wuce baka daukaka ‘kara ba toh hakan yana nuna ka amince da hukuncin Kotun farko, bayan kwana 14 sun wuce baka da ikon tuhumar wannan hukuncin.
~ Oral Adumbration in Appeals:
A Dokar Kotun ‘Koli da Court of Appeals idan ka daukaka ‘kara toh kana da damar bayar da bayani da Baki (Orally) wato Lauyoyin ka na minti 15 ne idan a Court of Appeal ne, idan kuma Supreme Court ne Mintoci goma ne.
~ Sannan Brief of Argument dinka kada ya wuce shafi 40 a rubuce. Replying Brief of Argument Kuma kada ya wuce 15 pages a Court of Appeal, shafi 10 a Supreme Court.
Kamar yadda aka sani, idan kaji ance Tribunal a Law toh Kotun wucin Gadi ne, wato temporary ne, bayan an kammala Shari’un zabe ake rushe su, sai bayan shekara hudu kuma, don haka basu da tabbatattun Alkalai ko Venue ko Ma’aikatan Kotu.
~ Alkalan akan dauko su daga wasu wurare ne daga manyan Kotuna bisa wasu ka’idoji na Supreme Court da Court of Appeals da sauran su.
Allah yasa mu dace….