ABINDA YA FARU A JIHAR ADAMAWA
Dazu gungun Mutane maza da mata manyan da kanana a birnin Yola jihar Adamawa sun fasa rumbun ajiyar abinci na Jihar Adamawa suja dasa wawa
Jami’an tsaro sun kawo dauki, kuma sunyi harbi, an samu asaran rayuka sosai
A halin yanzu Gwamnan jihar Adamawa Umar Fintiri ya ayyana dokar ta baci tare da hana fita na tsawon awa 24 a birnin Yola
To wannan abin tsoro ne, ya kamata wannan abin da ya faru a Adamawa ya zama babban darasi ga shugabannin Demokaradiyya a Nigeria, ya kamata wannan abin ya hanasu bacci, kar su sake bacci har sai sun samawa talakawa saukin rayuwa
Imba haka ba, ina jiye mana tsoron boren talakawa da kuma yunkurin haifar da juyin juya hali (Revolutionary) a Kasarnan, don haka masu rike da madafun iko su yi hankali
Talaka zai iya yin hakuri da komai amma banda yunwa, dole a samawa talaka sauki
Allah Ya sauwake