Labarai

Tirkashe Kotun Birtaniya Ta Tuhumi Diezani Kan Zargin Karbar Cin Hanci

Tirkashe Kotun Birtaniya Ta Tuhumi Diezani Kan Zargin Karbar Cin Hanci

Alison-Maduke ta rike mukamin ministar mai a zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan daga 2010 zuwa 2015.

 

WASHINGTON, D.C. —
Wata kotu a Birtaniya ta tuhumi tsohuwar shugabar kungiyar kasashe masu arzikin mai ta OPEC, Diezani Alison-Madueke da laifin karbar cin hanci a lokacin tana rike da mukamin ministar mai a Najeriya.

APPLY NOW!  Laifin Me Maryam Shatty Tayi Aka Cire ta a minista??

Hukumar da ke yaki da manyan laifuka ta NCA a Birtaniya ce ta bayyana hakan a ranar Talata.

“Muna zargin Diezani Alison-Madueke ta yi amfani da kujerarta a Najeriya ta karbi kyautar kudade saboda ta ba da wasu kwantiragi na miliyoyin fam,” In ji Andy Kelly da ke shugabantar sashen laifukan kasa da kasa a hukumar ta NCA.

APPLY NOW!  Hon, Mannir Babba Ɗan Agundi Yayi Nasara A Kotu Inda Ta Tabbatar Masa Da Kujeran Sa.

An ba da belin Alison-Madueke mai shekaru 63 tun bayan da aka kama ta a watan Oktoba a London a shekarar 2015.

A ranar 2 ga watan Oktoba ake sa ran za ta gurfana a gaban kotu a cewar NCA.

Lauyan tsohuwar ministar man ya fadawa AFP cewa Alison-Madueke za ta kalubalanci zarge-zargen da ake mata.

Alison-Madueke ta rike mukamin ministar mai a zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan daga 2010 zuwa 2015.

APPLY NOW!  Ana Shirin Tsige Shugaban Kasar America Joe Biden

Ta kasance mace ta farko da ta rike mukamin ministar mai a Najeriya da mukamin shugabar kungiyar ta OPEC.