Sojojin Nijar sun ɗauki mataki kan Najeriya
Gwamnatin mulkin soja a jamhuriyar Nijar ta yanke duk wata hulɗa da Najeriya bayan zaman masalaha ya rushe.
Wannan mataki na zuwa ne bayan shugaba Tinubu ya tura Sarkin Musulmi da Abdulsalami Abubakar, su gana da sojojin da suka kifar da gwamnatin Bazoum.
Rahoto ya nuna wakilan da Tinubu ya tura ba su samu ganin shugaban masu juyin mulkin ba, sai dai sun gana da wakilan soji.
A wata sanarwa da suka fitar, sojojin sun ce sun yanke hulda da Najeriya, Faransa, Amurka da Togo.
📷: Abdulfagge (Twitter)