Masarautar Gumel Ta Fitar Da Dokokin Mallakar Amarya A Sauƙaƙe
Masarautar Gumel dake Karamar Hukumar Gumel a Jihar Jigawa ta Fitar da Wasu Dokoki da ƙa’idoji na aure a yankin.
Wannan na ƙunshene ne cikin wata takardar sanarwa da aka fitar daga Masarautar Mai ɗauke da Sa Hannun Alhaji Murtala Aliyu dake Zama Sakataren Masarautar Gumel.
Inda Takardar ta Nuna Wasu Dokoki kimanin Goma Sha Tara da Masarautar ta ƙayyade kayan da Za a yi Amfani da Su na Aure da kuma bukukuwan Aure a yankin Masarautar Gumel.
Ga dokokin kamar haka:
1. Ba a ƙayyade sadaki ba amma dole ne ya dace da yanayin tattalin arziƙin al’umma.
2. Tufafi Shida (6).
3. Takalma uku (3).
4. Ɗan kunne da sarƙa uku (3).
5. Mayafi da hijabi uku (3).
6. Ɗankwali uku (3).
7. Kayan kwalliya saiti biyu (2).
8. Kada kuɗin kayan lefe ya wuce Naira Dubu Dari (100,000).
9. Maza ne zasu riƙa kai lefe.
10. An hana kawo kuɗin na-gani-ina-so
11. An hana kawo kuɗin sa rana.
12. An hana yin gara.
13. An hana yin kaɗe-ƙaɗen da Maza da mata zasu cakuɗa da juna.
14. Kada shagalin biki ya wuce 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.
15. Motoci uku (3) aka yarda su kai amarya.
16. Kai amarya kada ya wuce 6:00 na yamma.
17. An hana ƙauyawa night, Arabian night, Yoruba night da sauran su.
18. An hana hawan angwanci sai da izinin fadar masarautar Gumel.
Adam S Adam✍️