
Al’ummar Najeriya na fama da matsaloli na hauhawar farashi da tsadar rayuwa abin da wasu masu lura da al’amura ke nuna cewa jama’a na bin wasu hanyoyi domin su tsira da rayuwarsu.
Hukumar ƙididdiga ta ƙasar, NBS, har ta yi gargaɗi cewa hauhawar farashin kaya tana yin barazana ga tattalin arzikin ƙasar.
Gargaɗin ya biyo bayan yadda hauhawar farashin ke ci gaba da haɓaka, tun daga watanni huɗu da suka gabata, inda a wata na baya-bayan nan hauhawar ta kai kashi 25.8 cikin ɗari a watan Agusta.
Wannan ƙaruwa ta watan na Agusta ta kasance mafi yawa tun shekara goma sha takwas da ta gabata.
Hukumar ta ƙididdiga ta kara da gargaɗin, cewa wannan hauhawa na hana cigaban tattalin arzikin Najeriyar.
Ƙuncin rayuwa
A tattaunawarsa da BBC, Dakta Bashir Mohammed Achida, malami a sashin nazarin tattalin arziƙi da ke Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo a Sakkwato, ya ce a halin da tattalin arzƙin ƙasar ke ciki yana gamuwa da koma-baya ne abin da ke ƙara ƙuntata ga rayuwar ƴan ƙasar.
“Arziƙin jama’a na raguwa kullum suna faɗawa cikin tsananin talauci da kuma rashin rayuwa mai inganci,” in ji shi.
Ya ce, ”duk lokacin da aka samu hauhawar farashi arziƙin mutane da ƴan kasuwa da kamfanoni na raguwa ne.”
“Kuma idan abin ya ci gaba za a kai wani mataki da ƴan kasuwa da kamfanoni za su durƙushe. Jama’a su kasa tafiyar da rayuwa mai inganci domin karfin tattalin arziƙin ya karye. Ƙasa inda ta nufa durƙushewar tattalin arziƙi ne,” in ji malamin.
Shi ma wani magidanci Kwamared Ammar Aminu Fagge, da BBC ta tattauna da shi a game da halin rayuwar da ƴan Najeriya ke ciki a yanzu, cewa ya yi:
”Halin da ake ciki a Najeriya yanzu ya kai masifa saboda abin da mutum zai ci ya gagara.
Magidanci a gida zai fita bai san inda zai je ba abin da zai samo bai kai su ci abinci ba.
Mutane sun dawo cin yalo da da masara da ɗata domin kar su mutu,” a cewarsa.
Ya ƙara da cewa, yanzu ta kai ta kawo mutane suna shan ruwan zafi don su samu sauƙi a rayuwa kar su mutu saboda yunwa.
Ya ce, lamarin ya wuce dukkan yanda mutum yake tunani.
Ina mafita?
Kwamared ɗin ya ce hanya ta sassauci ita ce, gwamnati ta yi duk abin da za ta yi dala ta sauƙo saboda a cewarsa tashin dalar ne ya sa duk waɗannan abubuwan ke faruwa.
Ƙari a kan wannan shawara da za ta iya fitar da ƙasar daga cikin matsain da take cik na tattalin arziƙi in ji Dakta Bashir Mohammed Achida shi ne na farko, a bunƙasa kayayyakin da za a iya fitarwa waje wanda hakan zai sa kuɗaɗen waje su ƙaru a Najeriya.
Sannan ya ce hanya ta biyu kuma ita ce, a bayar da gudummawa ga kamfanonin cikin gida na ƙasar wanda hakan zai bunƙasa karsashi da ƙarfin gwiwarsu.
Gwamnatocin Najeriya a matakai daban-daban suna ta bayar da tabbacin bin matakan samar da sassauci, game da mawuyacin halin rayuwa da jama’ar ƙasar ke ciki.
To amma abin na zama kamar dukan kura da gwado, kuma matsalolin da ake fama da su a ƙasar, na ci gaba ba tare da wani sauƙi a zahiri da jama’a ke gani da ji a jikinsu ba da zai kwantar musu da hankali.