Labarai

Yan sandan sun gano mata 26 da ake shirin safara

Yan sandan sun gano mata 26 da ake shirin safara

Yan sandan Kenyan sun gano wasu mata ‘yan asaslin ƙasar Habasha har 26 da masu sarafarar jama’a suka kulle a wani kangon gida a tsakiyar garin Murang’a.

Jami’an tsaron ‘yan sandan sun kai samamen a daren ranar Litinin inda suka kutsa kai cikin ƙaramin gidan da aka tsare matan waɗanda suka shafe har tsawon mako ɗaya ba tare da shimfiɗar kwanciya ba face wata tsohuwar katifa ɗaya tal.

Rahotanni sun ce an yi safarar matan ne daga kan iyakar Moyale inda daga bisani aka tsara kai su Afrika ta Kudu.

‘Yan sandan sun ce sun samu nasarar kama su ne tare da karɓe musu fasfo da wayoyinsu na hannu.

An kuma samu nasarar kama wanda ke da gidan kazalika an ci gaba da neman sauran masu hannu a safarar mutanen.

APPLY NOW!  Yadda aka sace mata kimanin Arba'in a Borno