Labarai

Girgizar kasa ta kashe sama da mutum 820

Girgizar kasa ta kashe sama da mutum 820

Girgizar kasar ta yi kamari ne a wani yanki mai tsaunuka mai nisan kilomita 71 da garin Marakesh a cewar hukumar kula binciken yanayin kasa ta Amurka.

 

Da misaflin karfe 23:11 na agogon kasar ne watau karfe (22:11 GMT) girgizar kasar ta faru.

 

An kuma sake samun girgiza kasa mai karfin maki 4.9 bayan mintuna 19.

APPLY NOW!  Gobara ta hallaka sama da mutum 60 a Afirka Ta Kudu

 

An samu asarar rayuka a Marrakesh da garuruwa da dama a kudancin Kasar a cewar ma’aikatar cikin gida.

 

“A cewar wani rahoton yankin girgizar kasar ta kashe mutum 600 a larduna da kananan hukumomi da ke al-Haouz, Marrakesh, Ouarzazate, Azilal, Chichaoua and Taroudant,”

 

Sanarwar ta kara da cewa mutane 150 sun jikkata kuma na wuce da su asibiti

APPLY NOW!  Mayakan ISWAP na kwarara daga Sahel zuwa tafkin Chadi da Najeriya

 

Hotonan bidiyo da ba a tabattar ba a shafin X sun nuna gine ginen da suka lalace, akwai kuma wasu gine ginen da ke rawa da kuma titunan cike da baraguzai. Mutane suna guduwa cikin firgici kuma suna tafiya cikin kura.

 

Wasu gine gine a garin Marrakesh sun ruguje, kamar yadda wani mazaunin garin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

APPLY NOW!  Wani Bangare na kotun ƙolin Najeriya ya kama da wuta

 

Rahotanni sun ce mazauna yankin sun yanke shawarar zama a wajen gidajensu ko da an sake samun wata girgizar kasa mai karfin gaske.

 

Wani mutum a garin ya bayyana jin ” girgiza mai karfi” da kuma ”gine gine na motsi”.

 

” Mutane duk sun shiga wani hali na firgici da dimauta. Yara na kuka kuma iyaye sun firgita ,” Abdelhak El Amrani ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP .

APPLY NOW!  Innalillahi, Mawaki Dauda Rarara ya gamu da hatsarin mota a yau Juma'a.

 

Ya kuma ce an samu katsewar wutar lantarki da na layukan sadarwa na tsawon mintuna 10.

 

An ji girgizar kasa a Rabat babban birnin kasar mai nissan kilomita 350 da yankin da girgizar kasar ta yi kamari da kuma Casabalanca da Essaaouira.